Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba.
A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar na gwada karfin soji, wanda ke dauke da sunan shahidi Manjezi, makamai masu linzami daga kasa zuwa teku da kuma daga kasa zuwa masu cin dogon zango, matsakaici da gajere.
Ya kara da cewa: A cikin wannan atisaye a karon farko an harba makami mai linzami na Nawab da ke goyon bayan shamakin jirgin sama da jirgin ruwan shahidi Qassim Suleimani kuma sun samun nasarar cimma wurin da aka harba su.