Gwamnan babban bankin kasar Iran Mohammad Reza Farzin ya bada sanarwan cewa tsarin musayar kudi tsakanin bankunan kasashen Rasha da Iran ya fara aiki, kuma daga yanzun Iraniyawa da kuma mutanen kasar Rasha masu katunan bankin Shetab na Iran da kuma Mir na kasar Rasha zasu iya musayar kudade a tsakaninsu a ko wace kasa daga suke tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Farzi yana fadar haka a birnin Mosco a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa a halin yanzu harkokin kasuwanci ko masu bukatar kudaden tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu ba sa bukatar sayan dalar Amurka don yin haka.
Kasashen biyu dai sun dade suna fama da takunkuman tattalin arziki daga kasashen yamma, don haka wannan shirin ya fitar da dalar Amurka daga harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
A halin yanzu dai tasirin takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasashen biyu zai ragu so sai.
Sannan akwai yiyuwar wannan shirin ya yadu zuwa wasu kasashen yankin, wanda a hankali-a hankali zai sa amfani da dalar Amurka ya yi aruni a duniya.