Wasu masu amfani da kafafen sadarwa na Internet ko yanar gizo, su koka kan wayar aika wani abu ta dandalin Tiktok ko Instagram sai da manhajar VPN, saboda gwamnatin kasar bata son a yada zanga zangar da mutanen kasar suke yi dangane da hana amfani da hajabin musulunci a makarantun gwamnati.
Gwamnatin Ilham Aliyuf ta takaida amfani da yanar gizo a kasar ne saboda hana labaran zanga zangar mutanen kasar na hana yan makaranta mata a kasar sanya rufin gashin kansu a makarantun gwamnati a wannan makon. Kuma tuni an bada rahoton kama mutane akalla 37 saboda hakan.
A cikin yan kwanakin da suka gabata ne, a cikin watan Satumba gwamnatin Ilham Aliyuf ta sauya wasu dokokin kayakin makaranta inda suka hana karin wani abu akan wanda ma’aikatar ilmi ta sanar, dokar bai ambaci hijabi a fili ba, amma shi take nufi. Don bayan an bude makarantu, gwamnatin ta fara bincike don tabbatar da malamai da daliban makarantun gwamnati suna bin wannan dokar ko yaya.
A nan ne mutane suka hau tituna ko kuma suka je makarantu don nuna goyon bayansu ga yan makaranta da malaman da suka ki cire hijabansu a makarantun gwamnati. Gwamnatin Baku ta ce tana son ci gaba da kiyaye abinda ta kira tsarin da wai ba ruwansa da addini.