Ayatullah Sistani Na Kasar Iraq Ya Fitar Da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Ayatullah Musa Shubairi Zanjani

Babban marja'in addinin musulunci na kasar Iraki Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya aike da sakon ta'aziyyar rasuwar marja'i Ayatullah Sayyid Musa Shubairi Zanjani tare da
AYATULLAH ZANJANI DA AYATULLAH SISTANI

Babban marja’in addinin musulunci na kasar Iraki Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar marja’i Ayatullah Sayyid Musa Shubairi Zanjani tare da bayyana rashinsa a matsayin musifa mai radadi.

Ayatullah Sistani ya kuma bayyana mamacin malamin da cewa; ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne akan tafarkin ilimi da koyarwa, ya kuwa kasance daya daga cikin muhimman ginshikan cibiyar ilimin addini ta Hauza a birnin Qum.

Ayatullah Sistani ya kuma ce; Ayyuka da rubuce-rubucen da Marja’in ya bari za su ci gaba da zama masu kima kamar yadda manhajarsa ta ilimi za ta zama abin koyi ga ma’abota ilimi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted