Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce makiya Iran suna kokarin yin Karin gishiri game da karfin da suke da shi a matsayin wani bangane nay akin kwakwalwa da tunani.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da wasu jami’ai a jiya Laraba a birnin Tehran.
Jagoran ya ce a ko da yaushe makiya Iran suna kokarin sanya tsoro a cikin al’ummar kasar tare da tilasta mata ja da baya a fagen soji.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya ce manufar irin wannan Karin gishiri da makiya suke yi shi ne domin tasiri a cikin azama ta al’ummomi da sanya jin rauni a zukata, da kuma dakile himma da kwazo na al’ummomin duniya.
Jagoran ya ce Imam Khumaini wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya taimaka wajen kawar da tsoro daga zukatan al’umma tare da sanya kwarin gwiwa da imani da dogaro da kai a cikin zukatan al’ummar kasa.
A kan haka ya ce, yana da kyau a fifita dogaro da kai da azama a cikin dukkanin lamurra, wanda hakan shi ne zai maye gurbin tasirantuwa da duk wani Karin gishiri da makiya dangane da karfin da suke tinkahon cewa suna da shi.
Sannan ya jinjina wa shahidai da suka yi sadaukarwa a dukkanin bangarori domin ci gaban tsarin jamhuriyar musulunci da kuma gwagwarmayar yaki da zaluncin masu girman kai na duniya, kare mutunci da karama da matsayi na al’ummar musulmi da wurare na musulunci masu tsarki.