Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza

Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da kudirin firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye birnin Gaza, wanda ke zama matakin farko na wani gagarumin farmakin

Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da kudirin firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye birnin Gaza, wanda ke zama matakin farko na wani gagarumin farmakin soji da ka iya kaiwa ga mamaye daukacin zirin Gaza, a cewar wani babban jami’in Isra’ila.

Matakin ya biyo bayan tattaunawa sama da sa’o’i 10 da aka shafe ana yi tare da nuna wani gagarumin shiri na ci gaba da kai  hare-haren Isra’ila kan Gaza.

Jami’an Amurka sun ce shugaba Trump ya zabi kada ya shiga cikin lamarin, inda ya zabi barin Isra’ila ta yanke shawarar kanta.

A wani bangare na sabon farmakin da ke tafe, ana sa ran dakarun haramtacciyar kasar Isra’ila (IOF) za su ba da umarnin kwashe Falasdinawa kimanin miliyan 1 da ke zaune a birnin Gaza da yankunan da ke kewaye da su a halin yanzu.

A cikin wata sanarwa, ofishin Netanyahu ya bayyana cewa IOF za ta mallaki birnin Gaza, yayin ake ci gaba da fuskantar matsalar jin kai da Rashin abinci da Ruwan sha gami da maguguna da sauran kayayyakin bukatar rayuwa a dauakcin yankin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted