Dubban mutanen kasar Girka, a birnin Athen babban birnin kasar da kuma sauran manya manyan biranen kasar sun gudanar da jerin gwano na goyon bayan al-ummar Falasdinu.
A birnin AThen babban birnin kasar zanga zangar ta kasance tsakanin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin zuwa na HKI.
Banda kasar Girka a wasu kasashe kimani 60 a duniya an gudanar da zanga zanga irin wannan inda suke goyon bayan samarda kasar Falasdinu mai cikekken yenci, da kuma shefe HKI daga doron kasar.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne HKI ta fara kissan kiyashi a gaza bayan da kungiyar Hamas ta fara kai mata hare hare neman yenci. Ya zuwa yanzo sojojin yahudawan tare da taimakon Amurka da kasashen yamma daga ciki har da kasar Girma ta kashe Falasdinwa fiye da 80000, wasi kimani 8000 sun bace sannan wasu kumani 180,000 sun ji rauni.
Har yanzun da muke wannan maganar HKI tana ci gaba da wannan kissan kiyashi, a gaza da sauran yankun falasdinawa da ta mamaye.