Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji  Shugaban FCC

Mukaddashin shugaban hukumar daidaiton rabon muƙamai ta Ƙasa (FCC), Hon. Kayode Oladele, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ya samu kashi 56.3 cikin 100 na muƙaman

Mukaddashin shugaban hukumar daidaiton rabon muƙamai ta Ƙasa (FCC), Hon. Kayode Oladele, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ya samu kashi 56.3 cikin 100 na muƙaman gwamnatin tarayya da aka nada karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da Kudu ke da kashi 43.7 cikin 100.

Oladele ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron bita na kwana guda kan “Ƙarfafa Jagoranci da Gudanarwa Bisa Renewed Hope Agenda.” Ya ce wannan rabon yana nuna ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da adalci da daidaiton wakilci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A cewarsa, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma suna da ministoci mafi yawa, mutane 11 kowannensu, yayin da Arewa ta Tsakiya ke da 8, Arewa maso Gabas 7, Kudu maso Kudu 6, da Kudu maso Gabas 5. Bugu da ƙari, Arewa maso Yamma ce ke da yawan muƙaman jagoranci mafi girma (157), sai Arewa ta Tsakiya 139, da Kudu maso Yamma 132.

Ya tabbatar cewa hukumar FCC za ta ci gaba da bibiyar sabbin nade-naɗe don tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun samu wakilci bisa RenewedHope Agenda na Shugaba Tinubu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments