Araqchi: Mashigar Hormuz Ba Zata Dawo Yadda Take A Baya Ba

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Komawa ga yanayin da ake ciki kafin 28 ga watan Fabrairu a mashigar ruwa ta Hormuz ba zai

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Komawa ga yanayin da ake ciki kafin 28 ga watan Fabrairu a mashigar ruwa ta Hormuz ba zai yiwu ba, ba tare da la’akari da gaskiyar lamari ba

A lokacin ganawarsa da takwaransa na Qatar, Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana yayin da yake magana kan rashin tsaron da aka sanya a mashigar Hormuz sakamakon harin da sojojin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wa Iran, wanda aka yi shi da hadin gwiwar wasu kasashe a yankin, cewa ba zai yiwu a yi magana game da komawa ga lamarin kafin ranar 28 ga watan Fabrairu wannan shekara ta 2026 ba, ba tare da la’akari da hakikanin abubuwan da ke faruwa, laifuka da barnar da aka yi wa Iran ba.

Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, Fira Minista kuma Ministan Harkokin Wajen Qatar, wanda ke ziyara a Tehran don tattaunawa da manyan jami’an Iran kan huldar kasashen biyu da ci gaban yankin, ya gana da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi a yammacin jiya tare da musayar era’ayoyi kan batutuwa da dama.

A lokacin taron, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi maraba da ci gaba da rawar da kasashen yanki da makwabta ke takawa wajen bayar da gudummawa ga rage tashin hankali, yana mai jaddada cewa halin da ake ciki a yanzu ya samo asali ne kawai daga harin da sojojin Amurka da Yahudawan Sahayoniyya suka kai, da kuma ci gaba da matakan shiga tsakani da haramtacciyar Amurka, musamman toshe hanyoyin jiragen ruwa da ta’addancin tattalin arziki da ake yi wa Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted