Araqchi: Iran Tana Riko Da Hanyar Diflomasyya, Amma A Shirye Take Ta Sabi Makamai

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Akwai damar cimma yarjejeniya mai kyau… kuma Iran a shirye take ga shirin zaman lafiya da fuskantar yaƙi

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Akwai damar cimma yarjejeniya mai kyau… kuma Iran a shirye take ga shirin zaman lafiya da fuskantar yaƙi

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Kasarsa ba ta neman yaki amma tana shirye don hakan, yana mai nuna cewa, akwai damar cimma yarjejeniya mai adalci da daidaito a yayin tattaunawar Geneva.

A wata hira da ya yi da India Today a ranar Laraba, Araqchi ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya suna kokarin jawo Shugaban Amurka Donald Trump zuwa fadan soja da Iran, yana mai tabbatar da cewa babu wani zabi na soja don warware “batun makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya.”

Ya jaddada shirin Iran na amsa duk wata tambaya ko magance duk wata damuwa game da shirinta na makamashin nukiliya, muddin an girmama ‘yancinta na amfani da fasahar makamashin nukiliya cikin lumana.

Ya bayyana cewa cimma yarjejeniya mai adalci da inganci da daidaito mai yiwuwa ne, yana mai lura da cewa: Akwai dama a lokacin taron Geneva na cimma matsaya da aka amince da ita. Duk da haka, ya jaddada cewa kasarsa “ba ta shirye ta yi watsi da ‘yancinta” na fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted