Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen laifukan da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14
Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da kuma inda aka kwana a tattaunawar bayan fage da Amurka.
Haka nan kuma ya yi bayani akan matsayar Iran akan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Gaza, tare da yin kira da a kawo karshensa da kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin.
Haka nan kuma ya yi bayani akan yadda Iran take ganin za a iya warware matsalar mamaya a Falasdinu da ita ce yin kuri’ar raba gardaga da dukkanin Falasdinawa,musulmi kiristoci da yahudawa za su shiga a ckin tsarin demokradiyya.
A karshe bangarorin biyu sun jaddada muhimmanci tattaunawa a tsakanin addinai domin shimfida sulhu da zaman lafiya.