Arakci: Iran Tana Goyon Bayan Kafa Gwamnatin Da Za Ta Hada  Kowa Da Kowa A Syria

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa a tare da takwaransa na kasar Oman anan birnin

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa a tare da takwaransa na kasar Oman anan birnin Tehran ya bayyana cewa; Iran da Oman suna da matsaya daya akan batutuwa da dama a cikin wannan yankin  wanda ya kunshi tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Syria da kuma kafa gwamnati wacce za ta hada dukkanin kabilu da kuma mabiya addinai na wannan kasa.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi ishara akan taron kwamitin tattalin arziki na hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu wanda zai kasance a wata mai zuwa a birnin Muscat. Bugu da kari ya bayyana cewa an sami karuwar musayar cinikayya a tsakanin bangarorin biyu da ta haura dala biliyan 2.5 a cikin shekarar 2023.

A kan abubuwan da su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya, Arakci ya ce da akwai mahanga daya da kasashen biyu suke da ita akan wajabcin tsagaita wutar yaki a Gaza da kuma bude hanyoyin shigar da kayan agaji.

Akan kasar Syria kuwa bangarorin biyu sun yi kira da a kare hadin kan kasar Syria da kuma kafa gwamnati da za ta hada kowa da kowa.

Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya yi Allawadai da hare-haren da Amurka tare da Isra’ila suke  kai wa kasar Yemen.

A nashi gefen ministan harkokin wajen Oman Badr al-Bu Sa’id ya bayyana cewa sun cimma matsaya akan  bunkasa harkokin kasuwanci da kuma saukaka hanyoyin zirga-zirga a tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments