Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, mafi yawancin kasashen duniya sun yi Imani da ka’idoji na cin gashin kai da ‘yanci.
Abbas Arakci wanda ya gabatar da jawabi a wurin zaman majalisar zartarwa a yau Lahadi ya ce ya bayyana cewa a fagen diplomasiyya Iran ta dauki makamin dakile kokarin kasashen turai na sake dawu da takunkumi a kanta, ta hanyar aiki tare da kasashen Rasha da kuma China.
Haka nan kuma ya yi jinjina ga matakin bayan nan da kungiyar ‘yan-ba-ruwanmu ta dauka na nuna cikakken goyon bayanta ga Iran, yana mai cewa; Ana samun kafuwar sabon kawance a duniya, yayin da kasashen turai da wasu tsiraru suke a gefe daya, ita kuwa Iran da mafi yawancin kasashen duniya da su ka kunshi Rasha da China suke tare bisa aiki da ka’idojin ‘yanci da cin gashin kai.
Tun da fari Iran da hadin gwiwar Rasha da China sun aike wa da MDD wasika akan rashin halarcin matakin kasashen Faransa, Birtaniya da Jamus na kakaba wa Iran takunkumi.