Araghtchi : Tehran Da Beijing Na Yin Shawarwari Don Tunkarar Kalubalen Shiyya-shiyya

Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai lokacin da ya isa birnin Beijing ranar Juma’a bisa gayyatar da takwaransa

Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai lokacin da ya isa birnin Beijing ranar Juma’a bisa gayyatar da takwaransa na kasar Sin Wang Yi ya yi masa.

“Babban makasudin wannan ziyarar ita ce ta [taimakawa] tuntubar juna kan batutuwan da suka shafi bangarorin biyu, na yanki, da na kasa da kasa,” in ji shi.

Ya kara da cewa, Iran na ci gaba da tuntubar juna da kasar Sin game da dukkan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa, yana mai cewa, a ko da yaushe kasashen biyu na da kyakkyawar alaka, don haka ya kamata su ci gaba da yin hadin gwiwa kan batutuwa daban-daban.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, “A halin yanzu muna fuskantar wani yanayi mai ma’ana, yayin da yake magana kan ci gaban yanki da na duniya daban-daban.

Araghchi ya ce yana da matukar muhimmanci ga Tehran da Beijing su kara yin shawarwari don tunkarar kalubalen shiyya-shiyya da na kasa da kasa da ake hasashen a shekarar 2025, musamman wadanda suka shafi kwamitin sulhu na MDD.

A watan Maris din shekarar 2021 ne kasashen biyu suka rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta hadin gwiwa ta tsawon shekaru 25, a kokarinsu na karfafa kawancen tattalin arziki da siyasa da suka dade.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments