Aragchi Yana Gana Da Firay Ministan Qatar Da Jami’ar EU A NewYork

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da fray ministan kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani a birnin NewYork na kasar Amurka. Taron

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da fray ministan kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani a birnin NewYork na kasar Amurka. Taron ya auku ne a gefen taron babban zauren MDD na shekara shekara karo na 81 a yau Talata 22 ga watan satumban shekara ta 2026.

Banda haka ministan ya gana da tokwarorinsa na kasashen Italia, Antonio Tajani san a Swisszland Ignazio Cassis.

An bude babban taron shuwagabannin kasashen duniya ta shekara shekara karo na 81 a yau Talata, a babban cibiya ko helkwatan MDD  dake birnin New York na kasar Amurka. Tare da taken “Sake dawo da aminci, da kula da sauyi. MDD ga kawo”.

A wannan karon ma, gwamnatin kasar Amurka taki ta bawa wasu daga cikin tawagar shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan Visar zuwa birnin NewYork. Daga ciki har da wasu yan jarida.

Har’ila yau ministan ya gana da Jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na tarayyar Turai Kaya Kalass a gefen taron na MDD karo na 81. Wanda aka bude daga yau 22 ga watan Satumba har zuwa 28-Satumba na shekara ta 2026.

Ana saran shuwagabanni ko wakilan kasashen duniya 193 mambobin a majalisar zasu hadu a cikin makon don gabatar da jawabai da kuma ganawa da juna kan al-amura da dama a cikin sa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted