Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal bin Farhan a jiya Lahadi ya bayyana masa cewa ammfani da karfi kan mutanen kasar Yemen don tursasasu kan amincewa da abinda saudia take so ba zai taba samun nasara ba.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin JMI a shirye take ta shirya tattaunawa tsakanin kasashen biyu don kawo karshen zubar da jini tsakanin kasashen biyu. Ya ce ci gaba da yaki zai kare dagula al-amura ne kawai.
An fara yakin ne tun ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015, bayan shekaru 8 da yaki ba tare da samun nasara ba. Aka dakatar da budewa juna wuta na shekaru 4 sannan wuni yakin ya sake barkewa a ranar 12 ga watan Yulin wannnan shekarar tsakani kasashen biyu.
Ya zuwa yanzu yakin ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutanen Yemen a yayinsa wasu da dama suka ji rauni. Sannan wasu da dama suka zama yan gudun hijira.
Banda haka ita saudiya ma ta cutu kuma tana kara cutuwa saboda sojojin Yemen ta hana jiragen ruwa na kasar Saudia da Jiragen sama tashi. Sun kuma lalata kayakin kamfanin Aramco da dama.