Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da sanarwar yarjejeniyar Doha tsakanin gwamnatin dimokaradiyyar Kongo da ‘yan tawayen kasar na kungiyar M23
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo da kungiyar ‘yan tawayen kasar ta M23 a ranar Asabar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Guterres ya kara da cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta kuduri aniyar tallafawa kokarin samar da zaman lafiya, da kare fararen hula, da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, tare da hadin gwiwar hukumomi da kawayen kasashen yankin da na kasa da kasa.
Kafin hakan dai cimma yarjejeniyar ta samu karbuwa daga kasashen duniya, ciki har da Amurka, wadda ta tabbatar da cewa, shugabancin Qatar ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aiki da kuma goyon bayan warware rikicin cikin lumana.