Antonio Guterres Ya Yi Kira Ga Kasashe Masu Arziki Da Su Cika Alkawalin Da Su Ka  Dauka Akan Muhalli

Babban magatakardar MDD  Antonio Guterres ya yi kira ga kasashe masu karfin arziki da su cika alkawulan da su ka dauka na taimaka kasashe masu

Babban magatakardar MDD  Antonio Guterres ya yi kira ga kasashe masu karfin arziki da su cika alkawulan da su ka dauka na taimaka kasashe masu raunin tattalin arziki da kudade domin fada da illolin sauyin  yanayi.

Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar Lesotho ya kuma yi fatan cewa nan ba da jimawa ba nahiyar Afirkan za ta sami dawwamammiyar kujera a cikin kwamitin tsaro na MDD.

Babban magatakardar MDD dai yana ziyarar aiki ne ta kwanaki uku a yankin kudancin Afirka da a ranar Larabar da ta gabata ya ziyarci Afirka ta kudu. Daga can ne ya wuce zuwa kasar Lesotho mai makwabtaka da ita, inda zai yi kwanaki biyu. Wata karamar masarauta ce mai cike da duwatsu, inda zai ziyarci madatsar ruwa ta Katse da kasar take son cin moriyar ruwan da aka tara ta fuskoki mabanbanta.

A yayin taron muhalli na MDD da aka yi a Azerbaijan  a watan da ya gabata,kasashe masu karfin arziki sun yi alkawalin cewa a kowace shekara za su ware dala biliyan 300 domin taimakawa kasashe masu tasowa da suke fuskantar mastalar dumamar yanayin duniya.

An sami gibi a cikin kudaden da su kasashen masu tasowa su ka bukaci a rika ba su a kowace shekara da su ne dala tiriliyan daya.

“Wajibi ne ga kasashen masu  karfin tattalin arziki  da su cika  alkawalin da su ka yi na bayar da dala biliyan 300 a kowace shekara.” In ji Antonio Guterres.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments