Antonio Guterres Ya Yi Kira  Da A Kawo Karshen Danniyar Wata Kasa Akan Duniya Saboda Takama Da Karfi

Babban magatakardar kungiyar MDD, Antonio Gutress wanda ya gabatar da jawabi a ranar Alhamis din da ta gabata ya ce; Matsalolin da duniya take fuskanta

Babban magatakardar kungiyar MDD, Antonio Gutress wanda ya gabatar da jawabi a ranar Alhamis din da ta gabata ya ce; Matsalolin da duniya take fuskanta ba za a iya warware su ba ta hanyar danniyar da wata kasa guda daya za ta yi, ya zamana ita kadai ce take zartar da abinda za a yi.’

Antonio Guterres ya kuma kara da cewa haka nan kuma ba za a iya warware matsalolin na duniya ba ta hanyar da zai zama kasashen biyu ne za su raba duniya a tsakaninsu.

Da ‘yan jarida su ka yi masa tambayar neman Karin bayani akan abinda yake nufi, babban magatakardar kungiyar ta MDD, ya ce; A fili yake cewa za a iya tsinkayo yadda duniya za ta kasance a nan gaba da kasashen Amurka da China za su zama masu karfin tasiri. Idan har muna son duniya ta zama mai dawwamammen zaman lafiya, kuma a samu ci gaba, to dole ne mu goyi bayan yadda bangarori masu yawa za su zama suna bakin fada wajen tafiyar da harkokin duniya.

Antonio Guterres ya kuma ce; Rashin hukunta masu laifi ne babban dalilin da yake sa ana kara samun rikice-rikice a halin yanzu, wanda kuma zai share fagen duk wasu mabarnata masu karfi su yi abinda suke so a ko’ina.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted