Antonio Guteres Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Tashe-tashen Hankula A Kasar Syria

Babban magatakardar MDD, Antonio Guteres wanda ya yi ishara da halin da ake ciki a Syria ya kara da cewa; ya zama wajibi ga dukkanin

Babban magatakardar MDD, Antonio Guteres wanda ya yi ishara da halin  da ake ciki a Syria  ya kara da cewa; ya zama wajibi ga dukkanin bangarorin da suke fada da juna  da su yi aiki tare da manzon musamman na MDD akan Syria Mr. Geir Pederson domin ganin Syria ta cigaba da zama kasa daya dunkulalliya ba tare da tarwatsewa ba.

Babban magatakardar MDD ya kuma yi ishara da yadda rayukan dubun dubatar fararen hula suke fadawa cikin hatsari a kasar ta Syria, sannan ya kara da cewa, dole ne ga dukkanin bangarorin kasar su kare rayukan fararen hula.

Antonio Gutters ya kuma bayyana cewa Syria kasa ce mai tsawo tarihi da cigaba wacce abin takaici ne aga tana tarwatsewa a wannan lokacin.

 A cikin kankanen lokaci ‘yan ta’addar kungiyar “Hay’atul-Tahrirus-Sham” ta  kwace iko da garuruwan Idlib, Hama da kuma Halab.

Gwamnatin Syria dai tana tuhumar Turkiya da taimaka wa ‘yan ta’addar da suke kai hare-hare a cikin kasar da zummar tilastawa Damascuss ta bude tattaunawa da Ankara.

Sai dai shugaban kasar Syria Basshar Asad ya ce ba zai taba zaunawa akan teburin tattaunawa da Turkiya ba alhalin tana mamaye da wani yanki na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments