Shugaban hukumar gidajen radiyop da talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB), Peyman Jebelli, da shugaban sashen yada labarai na harsunan ketare IRIB World Service, Ahmad Noroozi a cikin jawabansu daban-daban sun yi ta’aziyyar shahadar jami’in hulda da manema labarai na kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta Lebanon.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Jebelli ya bayyana shahadar Mohammad Afif a matsayin gwarzo saboda gwagwarmayar da ya kwashe tsawon shekaru yana yi a fagen yada labarai wajen tinkarar gwamnatin sahyoniyawan.
A daren Lahadin da ta gabata, kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa an kashe jami’in huldarda da manema labarai a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a hedkwatar jam’iyyar siyasa ta Baath a unguwar Ras al-Naba da ke tsakiyar birnin Beirut.
Shi ma shugaban Hukumar Kula da watsa shirye shirye a harsunan ketare ta IranAhmad Noroozi, ya fitar da wata sanarwa don nuna girmamawa ga shugaban yada labaran Hizbullah da ya yi shahada, yana mai yabawa Afif a matsayin “tabbatacciyar hanyar bayyana ra’ayin gwagwarmayar Lebanon.
Shahidan ya yi aiki a matsayin “jarumi a kan hanyar gaskiya da gwagwarmayar inji Norrozi.