Daruruwan mutane sun fito kan titunan biranen Lazikiyya, Dardus, Husm da Hamah domin nuna kin amincewa da hotunan kona hubbaren shugaban mazhabar Alawiyya a garin Halab.
A jiya Laraba ne dai aka watsa wani faifen bidiyo da yake nuna masu dauke da makamai sun shiga cikin hubbaren Abu Abdullah Al-Husain Al-Khusaibi dake yankin Mislon na a gundumar Halab, suna cinna masa wuta.
Wannan lamarin dai ya faru ne a cikin wannan watan na Disamba mai karewa, a lokacin da ‘yan kungiyar “Tahrirus-Sham” su ka shiga cikin garin a hanyarsu ta kwace iko da birnin Damascus.
Daya daga cikin masu kula da hubbaren na Al-Khusaibi ya fada wa kafafen watsa labaru cewa, lamarin ya faru ne a wani lokaci a baya da masu dauke da makamai suke shiga cikin Halab, ba yanzu-yanzu ba ne.
Ya kuma yi ishara da cewa, an tuntubi shugabannin mazhabar ta Alawiyya da kuma sabbin masu mulki a kasar ta Syria domin hukunta wadanda su ka aikata wannan laifin da kuma kwantar da hankalin mutane. Haka nan kuma ya jaddada cewa watsa wannan faifen bidiyon a wannan lokacin manufarsa haddasa fitina.
Syria dai kasa ce mai cike da mazhabobi da ma addinai mabanbanta.