Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town.
Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa.
Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka.
Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da nadama ba.
Gwamnatin Trump ta kori Rasool sakamakon kalaman da ya yi a cikin shafukan yanar gizo, wanda gwamnatin Trump ke kallon kalamansa a matsayin batunci ga Amurka.
Korar Rasool, wanda tsohon mai fafutukar yaki da wariyar launin fata ne, ya kara dagula dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wadanda manufofin Trump na baya-bayan nan suka kara kawo tankiya da zaman doya da manja a tsakaninsu.