An Yi Taho Mu Gama Tsakanin ‘Yan Gwgawarmaya Da ‘Yan Mamaya A Nablus

A yau Jumaa ‘yan mamaya sun jikkata waji bafalasdine  yayin da su ka kutsa cikin garin Nablus dake yammacin kogin Jordan, kamar kuma yadda su

A yau Jumaa ‘yan mamaya sun jikkata waji bafalasdine  yayin da su ka kutsa cikin garin Nablus dake yammacin kogin Jordan, kamar kuma yadda su ka kama samarin Falasdinawa 50.

Hukumar agaji ta “Red Crescent” wacce ta fitar da wata sanarwa ta ce, ma’aikatanta sun yi wa wadanda su ka jikkata aiki bayan da aka harbe su da albarusai na gaske,sanadiyyar taho mu gamar da aka yi a  tsohon garin Nablus.

Kamfanin dillancin labarun Falasdinawa na ( WAFA) ya nakalto cewa; sojojin mamayar sun bude wuta da kuma jefa bama-bamai masu kara da hayaki mai sa hawaye akan Falasdinawa a kusa da sansanin ‘yan hijira na Bilata da kuma Askar.

Har ila yau kamfanin dillancin labarun na “WAFA” ya ambato wani shaidar ganin ido yana cewa, sojojin mamayar sun harbi wata mota akan titin Faysal da hakan ya yi sanadin illata ta.

Kakakin sojojin mamaya ya ce, sojojinsu sun kashe Bafalasdine daya a Nablus sai kuma wani guda a Kalkiliya.

A gefe daya, sojojin na mamaya sun ambaci cewa sun kama samarin Falasdinawa 50 a yankin yammacin Kogin Jordan a cikin makon da ya shude.

Magajin garin “Bait-Awa”  Muhammad al-Musalama, ya ce;sojojin mamayar sun kutsa cikin garuruwa da dama da motocin soja tare da yin kutse a cikin gidajen mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments