An Yi Bikin Ranar Al’adu Ta Birnin Shiraz A Kasar Tanzaniya 

An raya ranar al’adun mutanen Shiraz na kasar Iran a birnin  Darussalam” na  kasar Tanzania wanda ya sami halartar manyan baki daga cikin gida a

An raya ranar al’adun mutanen Shiraz na kasar Iran a birnin  Darussalam” na  kasar Tanzania wanda ya sami halartar manyan baki daga cikin gida a kuma waje.

Jakadan jamhuiryar musulunci ta Iran a kasar Tanzania, Husain al-wandi ya bayyana cewa, raya wannan ranar za ta kara karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu.

Shi kuwa babban jami’in Iran mai kula da al’adu a kasar ta Tanzania Muhsin Ma’arifi  ya ce; Zaman  mutanen Iran a cikin wannan kasa, ya sha banban da yadda ‘yan mulkin mallaka daga kasashen yammacin turai su ka yi, domin su turawa aikinsu shi ne kare manufofinsu na kashin kansu kadai.

Ma’arifi ya kuma ce; Mutanen Shiraz da su ka zauna a wannan kasar sun cakuda da ‘yan asalin ‘yan kasa da hakan ya kai ga samar da wata al’ada ta musumman, sannan kuma ya bunkasa tattalin arzikin mutanen yankin.

Daruruwan shekaru da su ka gabata mutanen Shiraz na Iran sun yi hijira zuwa gabashin Afirka, inda su ka cakudu da al’ummun yankin, da  kuma larbawa da  Indiyawa, da hakan ya kai ga samar da harshen Sawahili da kuma al’adu na musamman a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments