Adadin Falasdinawa da Isra’ila ta kashe tun daga ranar fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba ya zuwa yanzu, ya kai 37,124, yayin da wadanda suka jikkata ya kai 84,712, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta tabbatar a yau.
A cikin rahoton, ma’aikatar lafiya ta bayyana cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun yi kisan kiyashi sau biyar a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, inda suka kashe jimillar mutane 40 tare da jikkata wasu 814 na daban a yau Litinin.
An yi nuni da cewa, da dama daga cikin wadanda abin ya rutsa da su na ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, yayin da motocin daukar marasa lafiya da jami’an bayar da agaji suka kasa isa gare su.
A cikin wata sanarwa ta daban, ma’aikatar ta yi gargadin cewa tasha daya tilo da ke ba da iskar oxygen ga cibiyoyin kiwon lafiya da marasa lafiya a yankin Gaza na cikin hadarin tsayawa daga aiki a cikin sa’o’I masu zuwa.
A cewar sanarwar, hakan zai jefa rayukan marasa lafiya da dama cikin hadari, tare da yin sanadin lalacewar magunguna da ake adana su a cikin firji, wanda hakan sakamako ne na rashin man dizal da ake sanyawa na’urorin da ke samar da wutar lantarki a tashar iskar oxygen da na’urorin sarrafa magunguna.