An Sami Shahidi 1 A Gaza Da Kuma Jikkatar Wasu Da Dama Sanadiyyar hare-haren HKI

Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da hakan yake a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta wanda kuma yake daukar shahidai

jana'izarShahidai

Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da hakan yake a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta wanda kuma yake daukar shahidai da jikkata wasu da dama.

Rahotannin da suke fitowa daga yankin na Gaza suna cewa mutum daya ya yi shahada, yayin da wasu da dama su ka jikkata a yankunan al-Buraij,Nusairat, da Magraqah.

Bugu da kari hare-haren na ‘yan sahayoniya ya yi sanadiyyar jikkata wasu masu tsaron asibitin “Kamal-Adwan.” Da garin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza.

A tsakiyar yankin Gaza kuwa, sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren guda hudu akan gidajen mutane,kamar kuma yadda su ka kutsa da motocin soja cikin titin “Salahud-Din”.

A bisa kididdiga ta karshe akan shahadai, an bayyana cewa yawansu ya kai 73,110, sannan kuma wadanda su ka jikkata sun kai 173,599.

Tun da aka sanar da tsagaita wutar yaki a Gaza, zuwa yanzu babu wani lokaci daya da ‘yan sahayoniya su ka dakatar da kashe mutanen Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted