An Kashe ‘Yan Sudan Uku Tare Da Jikkata Wasu Bakwai A Kasar Sudan Ta Kudu

‘Yan kasar Sudan 3 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 7 na daban suka jikkata baya bullar tarzoma a birnin Juba fadar mulkin kasar

‘Yan kasar Sudan 3 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 7 na daban suka jikkata baya bullar tarzoma a birnin Juba fadar mulkin kasar Sudan ta Kudu

Majiyoyi daga birnin Juba sun shaida wa tashar talabijin ta Aljazeera a yau Juma’a cewa: An kashe ‘yan kasar Sudan 3 tare da raunata wasu 7 na daban sakamakon tashin hankalin da ya barke a babban birnin kasar Sudan ta Kudu, inda aka kaiwa ‘yan kasuwan Sudan hari, biyo bayan rahotannin da suke cewa an kashe sojojin Sudan ta Kudu a jihar Aljazira da ke tsakiya kasar Sudan a lokacin da sojojin Sudan suka kai hari da nufin kwato fadar mulkin jihar, birnin Wad Madani.

Majiyar ta kara da cewa: Mahukunta a Sudan ta Kudu sun dauki matakan kariya ta hanyar rufe kasuwar Kongo Kongo da ke birnin Juba da kuma kasuwar Al-Jaw da ke garin Wau, inda ‘yan kasuwar Sudan suka mallaki mafi yawan shaguna a garuruwan biyu.

A nata bangaren, fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu ta yi kira da a yi “hakuri tare da kai zuciya nesa, gami da bada dama ga gwamnatocin Sudan ta Kudu da makwabciyarta Sudan su warware wannan batu ta hanyar da tafi dacewa, a wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Alhamis.

Ta kara da cewa; “Bai kamata a bar fushi ya ruguza hukunci ba, kuma ‘yan Sudan din na sun gujewa kasarsu ce saboda tashin hankali don haka sun cancanci samun kariya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments