Jami’an yan sandan birtaniya sun kama wata babbar likita saboda matsin lambar da suka fuskanta ga masu kare Isra’ila, sakamakon yada bayanan yin tir da kisan kare dangi da HKI ke yi wa alummar gaza a kafafen sada zumunta.
Ellen Riesels kwararriyar likitan yara wadda ta kwashe shekaru 15 tana aiki a asibitin Whittington ta bayyana cewa jami’an yan sanda ne suka shigo har gidanta suka kamata, a gaban yayanta a ranar Asabar da ta gabata,
Dokto Rahme Al’adwan ya bayyana a shafinsa na x cewa Masu goyon bayan isra’ila sun fara addabar ta ne tun a watan satumba bayan bayyanarta a zanga-zangar nuna goyon bayan falasdinu,
Krisel it ace ta farko da aka kama bayan bayyanar ta dauke da kwali dake nuna goyon bayan Alummar falasdinu da kuma nuna adawa da kisan gare dangi da HKI ta yi a yakin Gaza, wanda a yan kwanaki aka dakatar da ita daga aiki a Asibiti, da kuma jingine lasisinta na tsawon watanni 9.
Kamun nata yana zuwa ne a daidai lokacin da yan sandan birtaniya suka yi barazanar kama duk wanda ya fadi Kalmar intifada a zanga-zanar nuna goyon bayan falasdinu, ko daga kwali dake dauke da Kalmar a rubuce,