An Ji Fashe-Fashen Wasu Abubuwa A Adis-Ababa Na Habasha

Rahotonni sun bayyana cewa: An ji fashe-fashen wasu abubuwa a babban birnin Habasha da daddare Majiyoyin diflomasiyya guda uku sun shaida wa Reuters cewa: An

Rahotonni sun bayyana cewa: An ji fashe-fashen wasu abubuwa a babban birnin Habasha da daddare

Majiyoyin diflomasiyya guda uku sun shaida wa Reuters cewa: An ji karar fashewar abubuwa cikin dare a babban birnin Habasha, Addis Ababa, yayin da wata majiya ta diflomasiyya da wani mazaunin wurin suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa: Wani fashewa ya faru a hedikwatar sojojin Habasha.

Reuters ta ambato wata majiya da ke da alaƙa da kawancen ‘yan adawa da ke fafatawa da sojojin tarayya a arewacin Habasha tun makon da ya gabata, tana cewa kawancen ya kai hare-haren jiragen sama marasa matuki ciki kan birnin Addis Ababa, ciki har da kai hari kan hedikwatar sojojin.

Masu magana da yawun fira minista, gwamnatin tarayya, da sojoji ba su amsa buƙatun kafofin watsa labarai na yin tsokaci kan batun hare-haren ba.

“Wani rahoto y ace: Sun ji hayaniya mai tayar da hankali na ‘yan mintuna, sannan wani fashewa ya biyo baya,” wani mazaunin babban birnin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa: Wata majiya ta diflomasiyya ta waje ta tabbatar wa AFP cewa an ji fashewar da misalin tsakar dare a hedikwatar tsaron ƙasa ta Habasha, amma ba ta iya tantance yanayin fashewar ko kuma wanene ke da alhakin ta ba.

Kanun Labarai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted