An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London

Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga

Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga asbitin saboda hatsarin samuwar wasu sinadarai masu cutarwa a cikinsa.

Jaridar da Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa , da masalin karfe 8.49 ne aka shaidawa jami’an kwana-kwana batun hatsarin, sannan a lokacinda suka karasa cikin asbitin sun yi kokarin samar da iska ne a cikin sa don baje sinadarai masu hatsari ga lafiyar mutane da suke zatun sun sulale sun shiga wurare da dama daban a cikin asbitin.

Labarin ya bayyana cewa na fidda mutane kimani 150 daga cikin asbitin. Kuma hotunan da aka watsa ta wayoyi sun nuna mutane a wajen asbitin kan Southwark, da kuma  Southeast London. A kusa da asbitin. Haryanzun dai babu rahoton wani ya jikata ko rasa rain.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted