Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta kakaba sabbin takunkumi kan bangaren manfetur na kasar Venuzwela da kuma iyalan shugaban kasar Nicolas Maduro da hakan ya shafi tattalin arziki, siyasa da kuma kara matsin lamba kan gwamnatin carakas.
Tattalin arzikin venuzuwela ya doru ne kan man fetur don haka sabon takunkumin kai tsaye zai cutar da gwamnatin maduro ne da kudaden shigarta na asali suna fitowa ne daga man fetur, gwamnatin Amurka ta sanar da sanya sabbin takunkumi kan bangaren man fetur din kasar Venuzuwel da kuma wasu mutane Ukku yan uwan matar Moduro,
Jaridar new york times ta fitar da rahoton cewa takunkumin na Amurka ya tilastawa gwamnatin moduro sayar da manfetur ta barauniyar hanya ta hanyoyin masu shiga tsakani da kuma tankomin mai, don haka shugaban Amurka Trump yayi amfani da wannan mataki wajen ci gaba da ikirarinsa na rusa gwamatin Muduro saboda zarginsa da fataucin miyagun kwayoyi,
Yanzu haka dai Amurka tana so ta yi amfani da matakin doka wajen kwace tankokin mai na kasar venzuwela , kuma ta sanya takunkumi ga kamfanonin mai guda 6 dake da kyakkyawar dangantata da safarar manfetur na kasar venuzuwela.