Amurka Ta Jinjinawa Najeriya Wajen Yaki Da Safarar Kwayoyi

kasar amurka ta yabawa najeriya kan yaki da muggan kwayoyi da ta ke yi.

Kasar Amurka ta jinjinawa hukumar NDLEA saboda rawar da ta taka wajen kama cibiyoyin samar da miyagun ƙwayoyi ta ƴan ƙasar Mexico a Najeriya da kuma hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Muƙaddashin Sakataren dake kula da yaƙi da miyagun ƙwayoyi na Amurka, dake kula da Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya, Michael Gonzales ya bayyana haka, lokacin da ya ziyarci shugaban hukumar Janar Muhammadu Buba Marwa mai ritaya a ofishinsa.

Gonzales wanda ya fara aiki a makonni huɗu da suka gabata, ya ce ya zaɓi Najeriya domin kai ziyarar ce a matsayin ƙasa ta farko saboda irin rawar da hukumar NDLEA ke takawa wajen dakile safara da kuma sarrafa ƙwayoyin da ake samu.

Jami’in ya ce ya je ƙasar ne domin ganin irin dabarun da hukumar ke yi wajen ganowa da kuma dakile masu aikata waɗannan laifuffuka waɗanda su ke daɗa nuna irin nasarar da hukumar ke samu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted