Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba

Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka

Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza.

Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya haifar da zaman dar-dar na wucin gadi, amma hakan bai canja yanayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba.

Ya ce makasudin ziyarar tasa ita ce fayyace dabarun Isra’ila, inda ya kara da cewa tattaunawa da Isra’ila ya zama dole domin fahimtar tsare-tsare a nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted