Amurka Ta Bukaci A Kada Kuri’a Domin Karfafawa Kudirinta Na A Tsagaita Wuta A Gaza 

Amurka ta sanar da cewa ta bukaci a kada kuri’a a kwamitin sulhu na MDD, game da kudurin da ta gabatar na neman Isra’ila da

Amurka ta sanar da cewa ta bukaci a kada kuri’a a kwamitin sulhu na MDD, game da kudurin da ta gabatar na neman Isra’ila da Hamas su gaggauta tsagaita wuta a Gaza.  

” Yau Amurka, ta bukaci kwamitin tsaron MDD, da ya shirya kada kuri’a game da daftarin da ta gabatar” kamar yadda mai magana da yayun tawagar Amurka a MDD, Nate Evans, ya fada a wata sanarwa.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga zangar goyan bayan falasdinwa a duniya da kuma neman Amurka ta kawo karshen goyan bayan da take baiwa Isra’ila.

Ko a ranar Asabar dubban jama’a ne a Amurka suka shiga wata zanga zanga gaban fadar White House, domin nuna goyan Falasdinu da kuma kin jinin halayyar mahukuntan kasar da suka ce suna da hannu a kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Ga masu zanga-zangar, shugabannin Amurka, musamman Joe Biden, suna da hannu a kisan kare dangi da aka fara watanni 8 da suka gabata.

A wani labarin kuma an yi irin wannan zanga zanga a titunan biraren Paris da Lyon na kasar Faransa.

Isra’ila dai na ci gaba da kai hare-hare Gaza da kuma Rafah, duk da kirare-kirayen da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa dama kotun duniya ke yi na ta dakatar da hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments