Shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya sami nasara a zaben shugabanci kasa na shekara ta 2024 ne saboda alkawalin kyautata tattalin arzikin kasar, a halin yanzu yana fama da matsaloli iri guda na wancan lokacin, amma mafi tsanani.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a lokacin kashe 80% na Amurkawa sun zabe shi saboda damuwarsu da tattalin arzikin kasar da kuma aljihunsu. Sai dai har zuwa yanzu wato a shekara ta 2026, wannan matsalar bata kau ba, sai dai ma ta kara tsanani saboda a mafi yawan mutane suna kokawa kan tsadar gasolin , wato makamashi wanda ya sauya rayuwar mutane. A farashi matsakaici ana saida gasolin kan dalar Amurka $4.36 kan ko wani galon. Dala $1.24 sun karu idan an kwatanta da na bara. Wannan inji hukumar AAA.
Wasu cibiyoyin bincike sun bayyana cewa, har yanzun maganar tattalin arziki ne zata mamaye zaben tsakiyar wa’adi a kasar ta Amurka don tsadar kayaki sune zasu hukunta wanda za’a zaba a cikin zabuka na watan Nuwamba.