Kungiyoyin kare hakkin bil’adama, da na lauyoyi da kuma masu ayyukan jinkai fiye da 100 ne a Amurka suka rubutawa shugaban Biden wasika inda suke bukace shi yayi watsi da kiraye kirayen wasu sanatoci na kakabawa jami’an kutun duniya ta ICC, mai makon haka ya goyi bayan kotun kan sammashin da ta fitar da kamawa da kuma gurfanar da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayyana cewa a cikin wasikar kungiyoyin sun bayyana a cikin wasikar kan cewa, idan shugaba Biden ya biyewa wadannan sanatoci, to babbar manufar gwamnatin Amurka ta kare raunana a duniya zata fadi kasa warwas, kuma wannan babbar illa ce ga manufofin Amurka a sauran kasashen duniya, musamman na tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasashen.
A ranar litinin da ta gabata ce Karen Khan babban mai gabatar da kara na kuntubn ta ICC ya fidda sammashin kama firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da wasu jami’an gwamnatinsa kan zargin aikata laifukan yaki a Gaza. Sannan kasashen Jamus, Faransa, Beljika da Slovakia sun bayyana goyon bayansu ga wannan matakin da kotun ta duniya ta dauka.
Bayan fidda wannan sammashin dai, shugaban Biden ya bayyana shi a matsayin zalunci ga Natanyahu. Sannan sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa fadda wannan sammashin zai iya shafar tattaunawar tsagaita budewa juna wuta tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da kuma HKI.