Amurka : FBI, Na Bincike Kan Wani Yunkurin Hallaka Trump A Jihar Florida

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta ce tana gudanar da bincike kan harin da wani dan bindiga ya kai a filin wasan golf

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta ce tana gudanar da bincike kan harin da wani dan bindiga ya kai a filin wasan golf na tsohon shugaban kasar Donald Trump a jihar Florida a matsayin “yunkurin kisa”.

Sashen yakin neman zaben Trump ya ba da rahoton harbe-harbe a kusa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican amma ya ce yana cikin koshin lafiya.

“Shugaba Trump na cikin koshin lafiya sakamakon harbe-harbe da aka yi a kusa da shi,” in ji wata sanarwa daga kakakin yakin neman zabensa Steven Cheung a ranar Lahadi.

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta ce, ta na gudanar da bincike kan abin da ake ganin na yunkurin kashe tsohon shugaba Trump ne.

Jami’an hukumar leken asiri ta Amurka da ke da alhakin kare shugabanni da tsaffin shugabannin kasar sun bude wuta bayan da suka ga wani mutum dauke da makami a kusa da gidan wasan golf na Trump da ke West Palm Beach a jihar Florida, a lokacin da yake wasan golf, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa Kamfanin Associated Press.

Harbin ya faru ne a filin wasan golf, kuma an tsare wani “mutum dauke da bindiga kirar AK47 mai gilashin hango nesa, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.

Shugaban Amurka Joe Biden da mataimakinsa Kamala Harris sun sanar da  “ji dadinsu” cewa Trump, yana cikin “koshin lafiya”, a cewar fadar shugaban kasar.

Ko A ranar 13 ga watan Yuli, hamshakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican a zaben da aka shirya yi a watan Nuwamba, ya ji rauni a kunnen sa ta hanyar wani harbin bindiga a wani taro a jihar Pennsylvania da ke arewa maso gabashin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments