Jaridar Isra’ila Ma’ariv ta bayyana cewa: Trump da Netanyahu sun kasa shirya sake daukan matakin yaki a kan Iran
Kafafen yada labaran Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun amince da gazawar makircin Netanyahu da Trump kan Iran.
Kamfanin dillancin labaran Mehr, wanda ya ambato Al-Mayadeen, ya ruwaito cewa: kafafen yada labaran Isra’ila sun amince da gazawar makircin Netanyahu da Trump kan Iran.
Jaridar Isra’ila Ma’ariv ta rubuta cewe: “Iran ta sami nasarar sanya ikonta a kan mashigar Hormuz cikin kwarewa, kuma yanzu Iran tana tsara yadda tattalin arzikin duniya zai kasance. Donald Trump da Benjamin Netanyahu sun gaza sosai wajen shirya yaki da Iran, kuma suna ci gaba da maimaita kurakurai iri daya a shirye-shiryensu na gaba.”
Avi Ashkenazi, mai sharhi kan harkokin soji na jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ya jaddada cewa: “Yaƙe-yaƙe biyu da Iran sun ƙare ba tare da cimma wani sakamako mai kyau ba, kuma Donald Trump da Benjamin Netanyahu sun gaza sosai wajen shirya wannan sabon yaki da Iran. Trump da Netanyahu har yanzu suna tsara tsare-tsare na gaba kan Iran, amma suna maimaita kurakurai iri daya a cikin wadannan tsare-tsaren.”
Kamar yadda kafar yada labaran Haramtacciyar Kasar Isra’ila Israel Hayom ta ruwaito, wani babban jami’i a cikin kungiyar ya bayyana cewa yakin da aka yi da Iran an yi shi ne don kifar da gwamnatin Iran, amma maimakon haka ya durkusar da gwamnatin Amurka.