Amurka : Ana ci gaba da zanga zanga bayan dan sanda ya harbe har lahira wata mata

A Amurka kisan da wani sandan shige da fice ya yi wa wata mata a yannkinMinneapolisdama goyan bayan da yake samu daga gwamnatin Amurka a

A Amurka kisan da wani sandan shige da fice ya yi wa wata mata a yannkinMinneapolisdama goyan bayan da yake samu daga gwamnatin Amurka a sahun gaba shugaba Donald Trump na ci gaba dashan martini.

Shi dai Trump da kusa duk makusantansa sun goyi bayan kisan da dan sanda ya yi wa matar ta hanyar cewa ya yi hakan ne domin kare kansa.

A shafukan sada zumunta musamman ”X” mabiya da dama da shahararru sun tir da kisan matar mai shekara 37 dake da ‘ya’ya uku.

Baya ga hakan kisan ya haifar da zanga-zanga a wurin, inda masu zanga-zangar suka yi Allah wadai da lamarin.

Magajin garin Minneapolis ya yi kira da a janye jami’an shige da fice na tarayya, yana mai cewa akwai damuwa game da tsaron jama’a.

Wani daga cikin ‘yan sandan shige da fice ne ya harbe har lahira matar a yankin Minneapolis na Amurka.

Aikin shige da ficen wani bangare na matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka kan shige da fice Amurka, wanda dama a cen baya ya haifar da tofin Allah tsine.

Jami’an tarayya, wadanda suka ambaci labarin, sun ce matar dake tukin wata mota ta nufi jami’an shige da fice, wanda hakan ya sa daya daga cikinsu ya bude wuta.

Lamarin ya faru ne yayin da aka tura dubban jami’an shige da fice na tarayya a yankin Twin Cities, a cikin abin da jami’an gwamnati suka bayyana a matsayin mafi girman aikin shige da fice da aka taba yi a Minneapolis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted