Ambaliyar ruwa ta lashe rayukan mutane fiye da 50 a yankin Tibesti da ke arewacin kasar Chadi
Sama da mutane 50 ne suka rasa rayukansu a kasar Chadi sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Tibesti da ke arewacin kasar wanda kuma ambaliyar ruwan ta fi shafa, yayin da aka shafe kusan mako guda ana ruwan sama a yankin.
Gwamnan jihar Tibesti, Mohamed Tochi Chidi, ya ce: Ambaliyar ruwa a yankin ta faru ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya tun daga ranar Juma’ar da ta gabata zuwa ranar Laraba da ta kai ga rushewar dubban gidaje da shaguna da yin awungaba da motoci.
Yana mai fayyace cewa: Adadin wadanda suka mutu ya kai mutane 54 sakamakon ambaliyar ruwar da ta mamaye yankuna shida na yankin Tibesti, kuma ruwan ya yi sanadiyyar korar mutane daga dubban gine-gine.
A cikin ‘yan kwanakin nan, ambaliyar ruwa ta addabi kasashe da dama a yammacin Afirka da tsakiyar nahiyar da suka hada da Guinea, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Cote d’Ivoire, Laberiya, Mali, Nijar, Najeriya da Togo. A cewar kididdigar Majalisar Dinkin Duniya, sama da mutane 700,000 ne masifar ta shafa gaba daya.