Search
Close this search box.

Al’ummar Yemen Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Yin Tir Da Gazawar Larabawa Na Kare Gaza

Al’ummar Yemen sun gudanar da gagarumar zanga-zangar yin Allah wadai da gazawar Larabawa dangane da laifukan yahudawan sahayoniyya a Gaza Al’ummar Yemen sun gudanar da

Al’ummar Yemen sun gudanar da gagarumar zanga-zangar yin Allah wadai da gazawar Larabawa dangane da laifukan yahudawan sahayoniyya a Gaza

Al’ummar Yemen sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna bacin rai kan yadda gwamnatocin kasashen Larabawa suka nuna gazawarsu wajen kare al’ummar Falasdinu daga bakar siyasa da zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, suna masu jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu musamman al’ummar da suke Zirin Gaza.

Zanga-zangar mafi girma an gudanar da ita ce a dandalin Al-Sabeen da ke birnin Sana’a fadar mulkin kasar, tare da gudanar tarurrukan gangami a dandali daban-daban a wasu jahohin kasar da dama, wadanda dukkaninsu suke rera taken yin Allah wadai da gazawar Larabawa da na Musulmi dangane da kisan gilla da kisan kiyashin da yahudawan ‘yan sahayoniyya suke yi a kowace rana ga al’ummar Falasdinu.

Ahmed Al-Ali, babban jami’in gudanarwa a kungiyar gwagwarmayar kudancin Yemen don tunkarar yaki da mamaya, ya bayyana cewa: Amurka tana goyon bayan duk wadannan laifuka da yahudawan sahayoniyya sukeaikatawa kan al’ummar Falasdinu kuma tana ci gaba da tallafa gwamnatin yahudawan sahayoniyya kullum rana wajen aiwatar da kashe-kashen gilla kan Falasdinawa.

Zanga-zangar kasar ta Yemen wacce take dauke da taken “Muna tare da Gaza da Al-Aqsa… Jihadi da tsayin daka har zuwa Nasara”, al’ummar sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da goyon bayan Falasdinu har sai an daina kai musu farmaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments