Al’ummar Turkiyya sun gudanar da zanga-zangar nuna fushinsu a gaban karamin ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Istanbul na kasar
Rahotonni sun bayyana cewa: Turkawa sun gudanar da zanga-zanga a gaban karamin ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin Istanbul, inda suka daga tutocin Falasdinu da kwalaye da aka rubuta kalmomin yin Allah wadai da zaluncin da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa Gaza tare da neman yanke huldar jakadanci tsakanin kasarsu da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Al’ummar musulmi na ci gaba da bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a daidai lokacin da al’ummomi suke ci gaba da nuna fushinsu kan laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da aikatawa. Dubban ‘yan kasar Turkiyya ne suka halarci zanga-zangar da aka yi a gaban karamin ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Istanbul, sannan a wani taro da kungiyoyin matasa suka shirya, sun daga tutocin Falasdinu da allunan rubutun yin Allah wadai da wannan ta’asa da kuma neman yanke alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya.