Search
Close this search box.

Al-ummar Musulmi A Amurka Sun Ce Idan Shugaban Biden Ya Sanya Hannu A Dokar tallafin Makamai Ga HKI Yayi Ha’inci

Kungiyar musulmi ta kasar Amurka ta bada sanarwan cewa idan shugaba Biden ya sanya hannu a dokar da majalisun dokokin kasar suka amince na tallafin

Kungiyar musulmi ta kasar Amurka ta bada sanarwan cewa idan shugaba Biden ya sanya hannu a dokar da majalisun dokokin kasar suka amince na tallafin makamai ga HKI ya ha’inci musulman kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu, majalisar wakilan Amurka ta amince da bawa HKI Karin tallafin makamai wadanda suka kai dalar Amurka biliyon 26. Sannan ana saran a cikin mako mai zuwa majalisar dattawan kasar zasu amince da dokar tallafin, sannan daga karshe shugaba Biden ya sanya hannu wanda hakan zai maida bukatar cikekken doka.

Kungiyar musulman ta bakin Robert Cauve ta bayyana cewa idan shugaba Biden ya sanya hannu a kan wannan dokar, wanda shi ne karshen goyon bayan da suke bashi a cikin harkokin siyasar kasar.

Wannan ba shi tallafin makamai wadanda gwamnatin Amurka take bawa HKI a yakin da take fafatawa da musulman gaza ba, sai dai duk tare da koma bayan da take fuskanta fiye da watanni 6 da fada yakin gwamnatin Amurka ta na tare da HKI a kissan kare dangin da take yi a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments