Al-Fayad: Rashin tabbas kan batun Siriya yasa dole a yi taka tsantsan da lamarin

Shugaban kungiyar Popular Mobilisation Forces (Hashd)  Faleh al-Fayyad, ya tabbatar da cewa rashin tabbaci kan batun Siriya yasa bukatar wajabcin yin taka tsantsan kan lamarin,

Shugaban kungiyar Popular Mobilisation Forces (Hashd)  Faleh al-Fayyad, ya tabbatar da cewa rashin tabbaci kan batun Siriya yasa bukatar wajabcin yin taka tsantsan kan lamarin, ya kuma jaddada cewa Dakarun Hashd sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana.

Babban kwamadan dakarun Hash Alshaabi na kasar Iraki, Faleh Al-Fayyad, ya tabbatar da cewa, rundunar Hashd ba ta fayyace wata matsaya ta karshe kan abin da ke faruwa a Syria ba.

A cikin jawabin da ya gabatar a wurin taron tsaro na mashahuran mutane da shugabannin kabilu na lardin Kirkuk, Al-Fayyad ya ce: “Ba mu jin cewa akwai kalubale kai tsaye ga Iraki, amma muna shirye-shiryen tunkarar kowace irin barazana a nan  gaba,” yana mai yi wa mutanen Siriya fatan samun kwanciyar hankali.”

Ya yi nuni da cewa “babu wanda zai iya cewa yana da kwarin gwiwa game da abin da ke faruwa a can,” yana mai nuni da cewa “ba a yi la’akari da ra’ayin Iraki game da abin da ya faru a Siriya a shekarun baya ba.”

Ya yi imanin cewa “faduwar rundunar sojojin Siriya da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kasar abin bakin ciki ne,” ya kara da cewa: “Ba ma tsoma baki cikin al’amuran al’ummar Siriya, amma Iraki da Siriya suna cikin wani yanki guda na tsaro.”

Al-Fayyad ya kara da cewa, “Ba ina shelanta yaki ko kuma  barazanar kai  hari ba ne, amma ina tabbatar da cikakken shirinmu.”

Ya kuma jaddada cewa, Popular Mobiliation Forces na karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar sojin kasar Iraki ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments