Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirummu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin nake kawo maku sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///…Madalla, idan masu sauraro suna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar ci gaban da aka samu a bangaren aikin likitanci da magunguna.
Mun bayyana cewa Ilmin likitanci, kamar sauran ilmomin da muka yi magana a kansu a cikin shirye shiryemmu da suka gabata, shi ma yana da matukar muhimmanci, kuma masana musulmi sun taka muhimmiyar rawa a bunkasa shi.
Mun kuma fara da hadisi wanda aka ruwaito daga daya daga cikin limamai masu tsarki daga manzon All..(s) inda yana fada a ma’anarsa:{ilmi kashi biyu ne, ilmin addinai da ilmin jikinkuna}. inda muka bayyana muhimmancin ilmin likitanci da kuma sanin magunguna a musulunci.
Mun bayyana cewa an fara bunkasa ilmin likitanci ne tare da tarjama littafai daga harsunan manya manyan kasashe a duniya zuwa harshen larabci. Musamman littafan Hippocrates da Galen.
Sai dai da dama daga cikin cututtukan da musulmi suka himmatu da samun magungunansu a lokacin, cututtuka ne wadanda suka shafi kasashensu, a kuma yanayin da wadanda kasashe suke ciki.
Kuma da dama daga cikinsu basu zo cikin littafan kasar girka wadanda aka tarjama ba.
A matsayin misali, Zakariyya Razi a cikin littafinsa mai muhimmanci mai suna ‘Kitabul Hawi’, ya gabatar da tsirrai masu maganin fiye da 700 , tare da ambaton amfanin ko wanne daga cikinsu, a magance cututtuka, tsirrai wadanda ba su zo cikin littafan likitanci na masana ilmin likitanci na girka da aka tarjama ba.
Al-hali, a cikin Hippocrates , masanin ilmin likitanci na kasar Girka a bangare tsirrai da magungunansu, bai kawo wannan adadin ba, ya kawo tsirrai 500 kacal.
Mun yi maganar littafin Hawi na zakariya Razi, mun bayyana cewa cututtukan da Razi ya kawo a cikin hawi, tare da bayanin magungunansu daban daban, sun dara na wadanda suke cikin littafin likitanci na ‘Hippocrates’ ko na Galen.
Sanna mun bayyana yanda Nestoriyawa suka kaura daga girka zuwa kasar Iran. Inda suka bukasa ilmin likitanci tare da bude jami’a da kuma makarantar koyon ilmin likitanci da sanin magunguna a Jundu-Shapoor. Sannan bayan bayyana musulunci wannan jami’ar ta taimaka wajen tarbiyantar da liktoci musulmi.
Sannan mun bayyana cewa akwai wasu gidajen da suka yi fice a ayyukan likitanci kuma sun hada da yan gidan Bakhteshoo.
Sannan Ibn Masuyyeh yana da rubuce-rubuce masu ban mamaki a cikin Larabci game da matsalolin kiwon lafiya da suka shafi nau’i zazzabi daban-daban, kuturta, baƙin ciki, cututtukan ido, da matsalolin abinci mai gina jiki.
Sai kumaAbul Husayn Ali ibn Sahl Rabban Attabari, wanda ya rubuta littafin ‘Firdaws al-Hikmah’, ya yi bayani game da hanyoyin maganin Girka, da na Romawa da kuma Indiyawa.
A cikin shirimmu na yau zamu dora daga inda muka tsaya. Mun bayyana cewa hadisin manzon All..(s) wanda ya rabi ilmi gida biyu, wato ilmin addinai da kuma ilmin jikina, ya kodaitar da musulmi neman ilmin magunguna don samun lafiyar jikunansu.
Don haka ilmin likitanci kamar ilmin taurari ne, wanda muka yi maganarsa a bayan. Yana da muhimmanci kwarai a rayuwar musulmi. Ilmin taurari yana taimaka masu wajen sanin lokutan sallolinsu, da eedunansu da kuma shekaru. Haka ma suna amfani da ilmin taurari don sanin inda suke a duniya da sauransu. Ilmin likitanci ma yana da muhimmanci sosai fiye da na taurari saboda da shi don lafiyar jikinsu ne.
Sai dai kamar yanda muka sani, masana ilmin likitanci sun maida hankali ne kan ilmin cututtukan da suka fi fama da su, saboda mai yuwa maguggungunan da suke bukata ba na cututtukan da suke fama da su ba ne.
Sau da dama ba’a rubuta magungunan cutar da ake fama da ita a kasashen musulmi a littafan da aka tarjama ba.
A matsayin misalin da mukaga batar Zakariya Razi ya kawo cututtuka da maganinsu har guda 700 a cikin littafinsa Hawi, al-hali Dioscorides wani masanin ilmin likitanci da magunguna na Girka ya kawo 500 ne kacal.
Hawi a cikin tarihin ilmin likitanci babu kamarsa. Don ya bayyana cututtuka dalla dalla. Ya kuma bayyana maganin ko wanne daga cikinsu. Wanda da wuya ka sameahi a littafn tarjamar Girka.
Sannan muna iya cewa a karshen karni na 3 hijiriyyah asasin binciken ilmin likitanci na Hippocrates da Galen sun zo karshe. Sai dai a dai dai lokacinne, wani nau’I kuma sabon ilmin likitanci wanda ake kira “Tibbun Nabawi’ ya bayyana.
Manufar bayyanar wannan sabon salon magance cututtuka shi ne bada dama ga sabon salon aikin likita wanda ba na masana girkawa ba gabatar da ayyukansa.
Wadanda suka rubuta irin wadan nan littafai malaman addini ne, tunda su suka san manzon All..(s). Suna ganin hanyar jinya ta amfani da ruwayoyin da aka karbo daga masu ruwaito hadisai daga manzon All..(s). da kuma ayoyin Alkur’ani maigirma yafi ra’ayin masana ilmin likitanci na girka.
A dai dai lokacin ne aka rubuta littafin ‘dibbul a’imma’. sannan a kasar Andulus kuma Ibnu Habib Andulusi ya rubuta littafi mai suna ‘Risalatun Mukhtasarah Fittibbi’. daga nan sauran masu rubutu kan wannan maudu’in suka dauko daga wajensu. Wanan salon ya sami karbuwa a karnuka na 7 da na 8 hijira kamariyya.
Abubakar dan Muhammad Zakiriya Razi, dan aslin kasar Iran, an haifeshi a shekara ta 251 bayan hijira, a garin Ray da ke kudancin birnin Tehran a halin yanzu. A lokacin garin ray shi babban birnin yankin, inda ake da makarantu da manya manyan malamai na addini da kuma ci gaban ilmin kimiyya.
A garin ne yayi karatun lissafi, taurari, adabin larabci, da ilmin likitanci, da falsafa.
Marubucin littafin ‘Uyunul Anbaa’ ya bayyana cewa a lokacinda Razi ya je birnin Bagdaza, yana dan shekara 30 da yan kai. Sannan an san shi da son karatu tun yana karami. Amma ya koyi ilmin likitanci, ya kuma zama malaminsa bayan ya girma. Kuma malaminsa shi ne Aliyu dan Raban Attabary.
A lokacinda ya kammala karatu ya dawo ray an bashi shugaban wani asbiti a garin. Yana aikin likitanci yana karantarwa. A cikin littafi mai suna ‘Tarihin Masu Hikima’ an kawo cewa, Razi shugaban wani asbiti ne a Rai, kuma yana karantarwa, daga baya an dauke shi zuwa shugabancin wani Asbiti a Bagdaza.
Wasu suna kiransa Galen na musulmi, kuma yana daga cikin manya manyan likitoci musulmi da aka yi bayan Abu Ali Sina. Ko Ibnu Sina. Zakariya Arzi yana ci gaba da rubutu da karatu da karantarwa har ya makance. Sannan mafi yawan ayyukansa na fasahar ilmin likitanci, wanda ya yi bincike ya kuma gano wa kansa ne.
A cikin tarihi ya zo kan cewa a lokacinda Sarki Adadu Addaulah Dailami yake son ya gina asbiti a birnin Bagdaza, ya bukaci a kawo masa likitan ya bashi shawara inda za’a gina asbitin. Sai aka kira masa Razi, wanda ya bada umurni a je a rataya masa manya manyan tsokan jan nama, a unguwanni daban daban a Bagdaza.
Bayan sa’o’ii 24 aka tattara masa su, sai ya zami unguwa wacce naman bai lalace ba, ko kuma ya ci gaba da zama cikin lafiya. Sai ya fadawa sarkin aka fara gina asbitocin.
Zakariyya Razi, likita ne wanda a ko yaushe yana son ya san abubuwa da kansa, ba tare da dogaro da ilmin masanan da suka gabata ba. Don haka yana da rubuce rubuce masu yawa a kan fannonin ilmin likitanci. A cikin wasu daga cikinsu ya sabawa wasu manya manyan likitoci kamar Galen na Girka.
Sun ce ya saba masa a matsaloli da suka shafi gani, jee da kuma jujjuyawar haske. Kuma ya rubuta littafai ko risalah fiye da 200, wadanda suka shafi Ilmin likitanci, magunguna, falsafah, hikimar dabi’ah, da taurari da sauransu.
Sannan a cikin wadan nan littafan, kimani 100 daga cikinsu kan ilmin likitanci da magunguna ne.
Littafin Hawi da kuma wanda yake kira Al-Mansuriy sune mafi muhimmanci daga cikinsu. A cikin littafin ya yi bayanin abinda ya lura da su a cikin ayyukan da yake yiwa marasa lafiyansa.
Wannan littafin ya fi ko wani littafin ayyukan likitanci a lokacin, kuma yafi tattara bayanan ayyukan likitanci a zamanin. A halin da muke magana kusan rabin wannan littafin yana nan.
Ya raba littafin gida biyu, bangare sanin ilmin kawai da kuma aiwatar da ayyukansa. Wanda ya zama kekyawar misalin ilmin likitanci ga wanda yake son koyonsa a lokacin.