Al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi 23

23-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni

23-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni Tahir Amin nake kawo mako sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun fara magana ilmin kanikanci a zamanin daulolin musulmi, har muka kai ga magana dangane da fasahar kanikanci, wadanda Al-Jazari ya samar, wasu kuma shi ya kirkirosu da kansa. Daga ciki mun bayyana cewa ya samar da agogo mai aiki da ruwa, wani mai aiki da makamashi. Sanan ya samar da inji wanda yake iya daga ruwa sama. Hakanan ya samar da kayakin aikin kanikanci masu yawa wadanda har a wannan zamanin da muke ciki ana amfani da su.

A cikin shirimmu na yau zamu kara da cewa, a cikin karni na 3 hijiri Kamari, ilmin kanikanci ya bunkasa a cikin duniyar musulmi. Sannan a farkon karni na 7 ilmin ya bunkasa har kuma ya kai kololuwansa. Masana ilmin kanikanci a lokacin sun sami nasarar samar da kayakin aikin kanikanci masu yawa.

Suna samar da duk wata bukatar al-ummar musulmi a lokacin,  tare da kayakin aikin da suka samar. Tare da amfani da wadannan kayakin aikin da suka samar. Suna samar da wadannan abubuwan daga karafa daban daban, wadanda suka hada da bakin karfe, zinari, azurfa, katako, gilashi, fata, ko auduna da zare ko audugan al-hariri ko kuma igiyoyin da aka samarwa daga itatuwa da sauransu.

Masana musulmi sun fi amfani da katako ko jan karfe wajen kere kerensu. Suna amfani da jan karfe ko copper don samar da pipe ko bututu,  kwalekwale  jikinkuna masu motsi. Har’ila yau suna amfani da jan karfe ko bakin karfe don samar da waya. Sannan suna amfani da waya wajen samar da sarka. Hakama suna yin hakoran taya ko manya manyan kwallaye daga katako ko karfe.

Daya daga cikin matsalolin da kasashen musulmi suka fi fama da su a lokacin shi ne karancin ruwa da kuma fari a wasu lokuta. Shaibi Mulayeem ya gabatar da wata dabara, wacce tare da ita, bayan an haka rijiya mai zurfi ana kawo ruwa kan doron kasa. Sai dai duk da haka a wasu wurare fito da ruwa daga kasa yana wuya sosai.

Daya daga cikin ayyuka masu amfani wadanda Jazri da kuma yan gidan Banu Musa suka samar a bangaren kanikanci, shi ne gina kayakin aiki daban daban don jawo ruwa sama daga cikin rijiyoyi, wanda suka suke kiransa na’urar jawo ruwa zuwa sama. Har yanzun ana samun na’urorin jawo ruwa sama irin na lokacin a wasu kasashen musulmi.

Yan gidan Banu Musa sune injiniyoyi na farko a cikin musulmi, wadanda suka bunkasa ilmin kanikanci a cikin duniyar musulmi. Littafi mai suna ‘Kitabu Hiyal Banu Musa’ shi ne littafi na farko wanda aka rubuta cikin musulmi dangane da ayyukan kanikanci. A cikin littafin sun bayyana kayakin aikin kinikanci har guda 100, mafi yawansu ana samar da su da amfani da dabarbarun kanikanci masu sauki ana iya samar da su. Daya daga cikin na’urorin da Banu musa suka gina shi ne famfun ruwa, wanda yake caccanza yanda yake watsa ruwa a lokacin bukatar hakan. Haka ma sun samar da wata na’urar mai fitillu, wanda kuma yake canza hasken ruwan da ke jujjuyawa kusa da su, a tsare.

Yan uwa Banu musa ne suka kere teburin kanikanci mai kwashe kasa, don aiki da shi wajen yashe kasa a kogi, ko bakin tekuna. Da wani fanka mai jan iska marasa kyau daga cikin rijiya duk suna daga cikin ayyukansu. Banda haka su suka samar da rodi ko Crankshaft wanda yake jujjuya hakoran tayoyi. Da Bawuloli masu mazugi, duk aikinsu ne.

Don haka banu musa, shekaru kimani 500 kafin turawa sun samar da lankwaceccen karfi wanda ake kira Crabkshaft suka kuma sanyasu cikin ingiju daban daban a zamaninsu.

Wasu daga cikin ayyukan Banu Musa sun hada da gina agogon ruwa, wanda yake amfani da nauyi ko takurawar ruwan da ke sama da agogin yake motsa shi. Sannan ya nuna lokaci. Irin wadannan agoguna an yi amfani da su a manya manyan birane, a kuma manya manyan filaye a cocuna a kasashen Turai, kafin su ci gaba. Wadannan agoguna a lokacin suna buga kararrawa a wasu lokuta na musamman.

Abulfatahi Abdurrahman Khazini, wani masanin ilmin kanikanci ne, kuma masanin ilmin kimiyyar lissafi sanenne a cikin ci gaban da ya kawo a ci gaban addinin musulunci a Trihi. Khazini ya bi hanyoyin Ibn Haitham da kuma Biruni a nau’in bincikensa na ilmin kanikanci, da haka kuma ya samar da ci gaba mai yawa a wannan fannin.

Khazini masani ne musulmi ya samar da abin gwada nauyi, wanda ake kira sikeli. Yana da wani littafi wanda ake kira Miaznunul Hikimah. Wanda ya kasance daya daga cikin muhimman littafai a ilmin kanikanci. Khazini a wannan littafin, ya kawo cewa ra’ayin malamai kamar Razi, da Biruni da ibu Haitham suna dai dai da ra’ayinsa ne. Kuma shi ne ya samar da na’urar gwajin nauyi ko sikeli, da na’urar daga nauyi, da agoguna, ma’aunin gishiri a ruwa, ko ma’aunin zafi da sauransu. Duk wadannan kirkiransa ne. Kuma ya kawosu a cikin wannan littafin, wanda duk wanda yayi karatu zai fahinta.

Aldomieli, wani malamin tarihi ne mutumin Italia.  Ya auna nauyin wasu abubuwa na musamman tare da amfani da nu’arar gwada nauyi wanda wanda Biruni da Khazini suka samar ya kuma rubutasu a cikin wani jadwali. Sannan ya sake gwadasu da wasu kayakin aiki, sannan ya kwatantau sakamakon ko wanne daga cikin. Sannan ya gano hakikanin nauyinsu. Khazini yayi nuni a cikin littafinsa yanda iska yake tajurawa jikinkuna, kokuma yake tasiri a kan nauyin jikunkuna, ya rika masana turawa irin su  Torricelli, Pascal, and Boyle sanin haka da karnuka kafin su gano hakan.

Sai kuam AbuAli Hassan dan Haitham Basri, wanda aka fi saninsa da Ibn Haitham. Masani ilmi lissafi kuma babban masani ilmi haske musulmi a cikin karni na 4 hijiri kamari.   Ibn Haitham yana da babban matsayi a ilmin kanikanci da kimiyyar lissafi, An san shi a cikin littattafan Latin ta Tsakiya a matsayin Alhazen.

Ya kamata a yi la’akari da Ibn Haytham a matsayin wanda ya fara jagoranci  a tsakanin masana ilmin kimiyyar gwaje-gwaje.

Domin ya kai da ra’ayoyinsa, musamman a ilmin sanin haske ne, ta hanyar gyaje gwaje.

Ibn Haitham ya sauya harsashen ilmin sanin haske, ya sauya tsarinsa yakyautata tsarin. Matsayinsa kamar Edison a ilmin kimiyar lissafi da kuma a fahinta da kuma a aikace.

Don bayyana haske ta tafiyarsa a mike, da kuma abubuwan da suke kebe duhu, ibn Haitham ya yi amfani da wuri ko daki mai duhu, ya kuma gudanar da gwaje-gwaje masu yawa.

Haka ma a dokokin jujjuyawar haske, ya gudanar da bincike masu muhimmanci, masu kayatarwa.

Ibn Haitham ya gudanar da bincike masu yawa dangane haske a gilasai masu kama da bututu da kuma masu kamanin kwallo. Yana ƙoƙarin auna girman ruwan tabarau masu faɗi ko a lanƙwashe, kuma ya wallafi littafai da dama a kan wannan fahintar.

Masana musulmi da kuma turawa sun tarjama wasu daga cikin littafansa a cikin karnin da ya gabata, sun kuma yada su.  

Ibn Haitham yana da wallafe wallafe da dama a ilmin kimiyyar lissafi da kuma sanin haske.

A cikin shekaru matsakaita, wato a lokacinda turawa suka fara farkawa, sun tarjama littafin ‘Nurul-Munazarah” zuwa harshen turanci, kuma littafin yayi tasiri mai yawa a ilmin kimiyar lissafi da kuma da ilmin sanin haske a kasashensu.

Kimiyyar sanin haske ta fara raguwa a cikin duniyar Musulunci, bayan Ibn Haitham saida ya kai ga manya manyan masana kamar Khoja Nasiruddin Toosi basu sanshi ba. Basu san gudumawarsa na ci gaban ilmi ba.  

Wannan halin ya ci gaba har zuwa karni na 7 hijiri kamari, Qutubud Deen Shirazi, wani masanin ilmin sanin haske, ya sake maida hankali kan wani bangare na ilmin sanin haske wanda ya sanya masa suna ‘bakin Gizo’ a nan Iran.

A yau, irin ci gaban da masana kasashen yamma suka samu, a wani bangare mai yawan sa, ya ginu a kan ayyukan Ibn Haitham ne.    Da wannan dalilin ne a kasashen yamma ake lakabi wa Ibn Haitham da ‘baban ilmin sanin haske’.

Wasu masana tarihi sun tabbatar da cewa ci gaban da aka samu a fannin sanin ilmin haske a kasashen Yamma, musamman A Jami’ar  Oxford, ya faru ne sakamakon, sanin da Turawan Yamma suka yi da ka’idojin Ibn al-Haytham na ilmin haske.

Don haka, wasu masana, sun ce, babu shakka kan cewa Roger Bacon, shahararren masanin ilmin falsafa kuma ilmin kimiyyar haske baturen Ingila, ya  tasirantu sosai da ayyukan Ibn al-Haytham.

A fannin kimiyyar lissafi da kanikanci, muna iya cewa masana musulmi sun maida hankali a kan fasahar ilmin haske fiye da ko wani fanni. Kuma sun sami ci gaba mai yawa cikinsa.

Har’ila yau muna iya kammala da cewa,  idan muna son mu fahimci nasarorin da masana Musulmi suka samu a wannan bangaren, to  dole ne mu yi nazarin irin ƙoƙarin da suka yi a fannonin kimiyyar lissafi da kanikanci

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted