Al-adu da ci gaban addinin musulunci a Tarihi 20

20-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni

20-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni Tahir Amin nake kawo mako sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar Khawarizmi wani babban malami ilmin lissafi musulmi ba’irane  ya gano ko ya kirkiro wasu ilmomi a wannan fannin wanda ya zama harsashen gina ilmin injina na wannan zamanin.

Khawarizmi ya gani ilmin lissafin muthallathat, da ilmin Algebra, wadanda bayan tarjamarsu zuwa harshen turanci, turawan sun yi amfani da shi wajen samar da ci gaba mai yawa a fagen ayyukan kanikanci da kare kare.

Mun bayyana cewa ana mafani da littafinda Khawarizmi ya rubuta a ilmin Algorism har zuwa karni na 16 miladiyya. Mun bayyana cewa, littafan da malaman musulmu suka rubuta, musamman a fannin ilmin lissafi sun taimakawa turawa da dama wagen bunkasa ilmi da kuma kaiwa inda suka kai a ilmin zamani.

Bayan Khawarizmi, an yi wani wamali musulmi mai suna Ibrahim Aqliidisi wanda ya ci gaba da bunkasa ilmin lissafia. IbrahimAqleedisi ya kirkiro wani tsari na warware matsalolin lissafi na kasa da daya. Shi mutumin birnin Damascus na kasar Siriya ne, ya kuma sami nasarar gani yanda za’a yi lissafin Aashaar, ko kuma lissafin al-amura kasa da daya. Kuma ya rubuta littafi a kan haka ya kuma kirashi da suna ; Lissafin Indiua” ya kawo wannan ilmin da ya kirkiro, ya kuma bayyana yanda za’a yi lissafinsa dalla dalla.

A lokacin rayuwar Ibrahim malamai da dama basu san amfanin ilmin da ya gano ko ya gano ma, lissafin Aashaaar ba, amma a bayansa da kimani shekaru 15. wani malami masi suna Ghiyathu Addin Jamshidi ya sake gabatar da wannan fahintar tasa.

Sai kuma Musa dan Shakir wanda shi ma yaye fice a ilmin lissafi da shi da yayansa sun gudanar da bincike mai yawa a cikin ilnin lissafi wanda a cikin karni na 3, bayan tarjamarsu turawan yamma sun amfana da wannan ayyukansu.  

Har’ila yau yayan musa sun gano yanda ake lissafin farfajiyar da’ira ta wata sabuwar hanya. Banda haka sun gani yanda ake samar da masaha ko fadin da’ira tare da la’akara da qatar, ko kuma layi daga tsakiya zuwa karshensa.

Sai kuma AbulHassan Thabit dan Qurrah, wanda shi ma ya taka rawar a zo a gani wajen bunkasa ilmin lissafi a cikin musulmi. Shi mutumin Harran ne, dake kasar Turkiyya a halin yanzu. An haife shi a shekara ta 211. ya iya harsuna siryananci, ibranci sannan ya taimaka wajen bunkasa ilmin lissafi a cikin musulmi a lokacin. Littafansa sun nuna yanda yayi aiki sosai a lissafin girma da fadin jikunkuna.  Har yanzun akwai littafansa da na wasu masana ilmin lissafi girkawa wadanda ya tarjamasu zuwa Arabia.

Sai kuma Abu Sa’id Sijizi, wanda shi mutumin Sistan ne, ya kuma rayu a karni na 4 kamariyya ya kuma hada zamani da Abu Raihan Biruni.   Sijizi ya kware a ilmin lissafi, kuma saboda haka Abu raihan biruni ya ambace shi a cikin littafinsa. Ya kuma bayyana cewa Sijizi ya warware  wasu matsalolin ilmin handasa ta wasu hanyoyi wadanda ba’a saba ba.  Yana da littafai kimani 45 da ya rubuta, kimani 34 daga cikinsu suna magana ne kan ilmin lissafi, sannan sauran kuma suna magana kan ilmin taurari da hukunce hukuncesu da kuma kayakin aiki na lissafin taurari.

Sannan har zuwa yanzun, duniya bata manta da Abu Raihan Biruni ba, wato fitaccen malamin taurari wanda ya rayu daga tsakiyar karni na hudu zuwa farkon karni na biyar kamariyya. An haife shi a shekara ta 362 kamariyya a garin Taath cikin lardin kuma babban birnin Khawarism Shahiyan.  Ya rubuta littafai da dama a fannonin lissafi, taurari, Jografiyya da kuma ilmin hako ma’adinai.

Ya rubuta littafai fiye da 180 da kuma tarjama da guntayen rubutu wadanda  suka shafi ilmin lissafi, taurari, da wasu bincike bincike wadanda suka shafesu.

Sai dai abin bakin ciki, ba’a tarjama littafan Abu-Raihan biruni zuwa harshen turanci daga larabci ba, kuma daya daga cikin littafansa masu muhimmanci shi ne ‘Tafhim’. wanda ya gabatar da fahintarsa dangane da ilmin lissafi Jabr da kanikanci. A cikisa ya ambaci yanda ake lissafin jikinkuna da nauyinsu. Sannan yana da wasu karatuttukan kan lissafin kusruwowi.

Yanzun kuma sai Abu Ali Sina, wanda ya rubuta littafai ko yayi bincike masu yawa a fannonin Falsafa, Likitanci, lissafi, taurari da sauransu.  An haifi Abu Ali Sina a kusa da garin Bukhara dake cikin kasar Uzbekistan a halin yanzu a shekara ta 370 kamariyya. Ya karnci mandiki, da likitanci da lissafe lissafe a garin Bukhara. Ta yanda yana dan shekara 17 a duniya ya yi jinyar Nuhu dan Sarki Mansur Samuni ya kuma warke. Bayan ya shahara da aikin likitanci, daga karshe ya sami damar shiga dakin ajiyar littafai na sarki Mansur Samani.

A lokacin ne Abu Ali Sani ya fara gudanar da bincike da kuma musayar ra’ayi da malaman da suka hada zamani da shi kamar Abu Raihan Biruni, Abu Nasr Araqi a fagagen ilmomi da dama, wanda suka hada da lissafi. Wannan babban malamin ya gabatar da ilmi mai yawa ga duniya a cikin wallafe wallafensa.

Daya daga cikin muhimman littafan da Abu Ali Sina ya rubuta sun hada littafin Shifaa. Inda ya yi maganar kanikanci, lissafi ko hisabim wake, da bincike da sauransu. Har’ila yau ya kawo batun al-amuran da suka zama lazimi mai karatun ilmin lissafi ya sansu ya kuma fahincesu. Abu Ali Sina ya yi maganar lissafin adadi da kebantattun usulansu.

Banda haka yana da wani littafi mai muhimmanci a kan aikin likitanci, musamman abinda ya shafi tiyata, da magunguna da ayyukan jinya dasauransu mai suna Kanun. Malaman tarihi sun bayyana cewa, bayan tarjana kanun zuwa harshen turancim an ci gaba da dogaro da littafinsa a makarantu da Jami’oin kasashen turai na karnuka masu yawa kafin su sauya shi.  

Sai kuma Khayyam Nishaburi, daya daga cikin fitattun malamai masana ilmin lissafi wanda kuma ya gabatar da ilmi mai yawa a wannan fannin. Sunansa shi ne Umar Khayyam Nishaburi. Ya yi fice a ilmin taurari da sararin samaniya a cikin rabin karni na biyar da kuma farkon karni na shida hijira kamariyya. Sannan mafi muhimmanci a cikin bincikin lissafi da yayi shi ne kan ilmin Jabr-Da mukabalah.

Sai kuma Khoja Nasiruddeen Tusi, wanda shi ma ya yi zurfi cikin ilmin lissafi da Hisabi. An haife shi a ranar 11 ga watan Jamada Aula na shekara ta 597H.K. agarin Toos dake arewa maso gabacin kasar Iran a halin yanzu.

Khoja nasiruddeen ya fara da karatun addini a gaban mahaifinsa wanda babban malamin addini ne a lokacin. Sannan ya shiga karatun hikima da ilmin masu dangantaka da hankali da tunani, wadanda suka hada da ilmin lissafi da ilmin tabi’a.

Khoja yana matashi ya fara karatun lissafi a gaban malaminsa Kamaluddeen a birnin Nishabur.  Daya daga cikin manya manyan ayyukan Khoja su ne gina dakin hangen sararin samaniya wanda ake kira Maragheh a a cikin garin mai sunansa a lardin Azrbaijan ta gabsa dake arewa maso yammacin kasar Iran a halin yanzu a shekara 657 kamariyya.

Bayan haka Khoja ya tattara manya manyan masana ilmin lissafi da taurari na zamaninsa a dakin na’urar hangen sararin samaniyarsa. Daga nan sai ya gina dakin karatu ko ajiyar littafai saboda karatu da bincike ga daliban ilmi gaba daya a ko wani fanni sukeso. Ya kuma wallafa littafai a fannonin ilmi da dama, wanda ya taimaka wajen yada ilmi a cikin al-ummar musulmi.

Khoja Nasiruddeen Tusi, karshen rayuwarsa ya kome garin muraghe inda yake ci gaba da wallafe wallafe littafai da kuma neman ilmi. Dangane karshe Khoja ya rasu a ranar 18 ga watan Zulhajji shekara ta 672 ya rasu a unguwar Kazimain na birnin Bagdaza a kasar Iraki.

Sai kuma Ghiyathuddeen Jamshidi Kashani, wanda shima ya yi fice a sanin ilmin lissafi a zamaninsa. Ya shahara da wallafe wallafensa a fannin ilmin taurari, ya kuma kirkiro kayakin aiki na gwaje gwajen a ilmin taurari a lokacin.

Wasu malaman taurari a kasashen turai suna ganin kayakin gwaje gwaje wadanda Kashani ya kirkiro sun fi inginci da lissafi dai dai a kan wadanda suke da su.

Ghiyathuddeen Kashani ya rasu a kimanin shekaru 824 kamariyya a garin samarakanda a lokacinda yake aikin kula da dakin na’urar hangen sararin samaniyar garin.

Daga cikin ayyukan sa yana lissafin fadin da’ira da wata hanya tasa mai bada lissafi dai dai.

Wannan hanyar lissafin nasa ya ci gaba da zama mafi inganci har zuwa shekaru 150 bayansa. Yana da wani littafai mai suna risalatul Muhidah” kan ilmin lissafi. Ya kammala rubta littafin a shekara ta 827. A halin yanzu akwai kofin wannan littafin a gidan ajiyan littafan tarihi a haramin Imam Ridha (a) a birnin Mashad na arewacin kasar Iran.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

===============================.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted