Al-Adu da ci gaban addinin Musulunci a tarihi 18

18-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na Al-adu da  ci gaban addinin musulunci a tarihi, shirin da ke

18-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na Al-adu da  ci gaban addinin musulunci a tarihi, shirin da ke kawo muku irin ciki gaban da addinin musulunci da musulmi suka samu tun bayan bayyanarsa zuwa yau, wanda ni Tahir Amin nake kawo muku sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauroro zasu kasance tare da mu a wanan makon.

///…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu, a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da magana dangane da dakunan ajiyar littafai ko dakunan karatu a cibiyoyim ilmi da kuma masallatayya a daular musulunci, mun kuma yi magana kan yanda bayan da daular musulunci ta rarraba cibiyar yada karatu ya yada zuwa wasu yankunan wadanda suka hada da birnin Al-Kahira na kasar Masar karkashin daular Fatimawa, kamar yadda aka gina makarantun Nizamiya a birnin Bagdaza, da farko.

Mun bayyana cewa Nizamulmulki ne ya samar da Nizamiyya ta farko, inda ya gina ta a matsayin makaranta a matsayin makaranta a mataki na karshe ko kuma Jami’o’ii kamar yanda muke kiransu a halinzu.

Inda ya samarda azujuwa da kuma manya manyan gidaje na malamai, sannan ya gina babban masallaci, kusa da shi ya gina babban dakin karatu. Kuma manya manyan malamai kamar Abu Ishaq Sirazi, da kuma Imam Algazali sun karantar a makarantar na wani lokaci.

Mun bayyana cewa, makarantar ta nizamiyya ta shahara ne saboda irin zurfin binciken ilmin da ake tattaunawa cikinta. Sai kuma a wani bangaren, ganin daular Fatimawa ko masu bin mazhabar Ismailiyya a Jami’ar Al-Azhar suna yada mazhabar shia, sai suka maida makarantar nizamiyya ta Bagdaza ta zama mai yada akidun mazahar sunna.  

Hakama suka maida wasu cibiyoyin Nizamiyya a Khurasan, da  Iraki su zama cibiyoyi masu yada akidun da sarakunan daularsu suke kai.

Da farko  dai an takaita maddojin da ake karantarwa a Nizamiyar zuwa Fikihun mazhabar shafi’iyyana da kuma hadisai da kuma karatun alkur’ani mai girma. Amma daga baya an shigoda da ilmomin Fikihu mai fadi, Asul da Hadisi tafsiri da kuma ilmin al-kur;ani, kalam da lissafi da ilmin likitanci da sauransu.

Marubucin littafi mai suna “wasiyoyin Nizamul Mulki: ya kawo sunayen sunayen mutane 85 a matsayin malamai a makarantar Nizamiyya na Bagdaza. Daga cikin sunayen da ya kawo har da Abu Adullahi Tabari, (495)q, da Abu Hamid Mohammad Algazali (505)Q Abu mohammad Khawarizmu (568) Q.

Sannan irin maida hankalin da Nizamul Mulki da sarakunan Sulujakawa suka yiwa birnin Nishabur a lokacin ya kai ga sun bunkasa Nizami da wurin. Makarantar ta yaye manya manyan malamai, Nawabigai, karkashin renon nizamiyyar Nishabibur wadanda suka hada da Hakim Umar Khayyam, da Imam Muwaffaq Nishaburi da Imamul Haramai, da AttarNishaburi da sauransu.

Ilmi ya bunkasa a makarantar Nishabur, saboda suna da manya manyan malamai kwararru kuma fitattu wadanda  suke karantarwa a makarantun na su. Wanda hakan ya Nishabur tana da matsayin na biyu bayan ta Bagdaza. Har’ila yau Nizamul Mulki ya gina irin wannan makarantar a birnin Esfahan, inda nan ma ya samar da fitattun mashahuran malamai masu karantarwa a makarantar. Sannan wannan ya sanya samuwar wannan makarantar ya maida Esfahan a matsayin daga daga cikin manya manyan cibiyoyin ilmi a cikin daular musulunci.

Daga cikin malaman Nazamiya na Esfahan akwai, Abubakar Mohammad ibn Thabit Khujandy (483) Q, sai kuma Fakhruddeen Abul-Alay Warkani. (559) q.

Sai kuma Nizamiyya na garin Balkh wacce take da fitattun malamai kamar Adam bin Asad Saharvardy. Sannan makarantar ta yaye dalibai kamar Rasheed Vatvat. Birnin Basra ma tana da makarantu irin wannan.  Kuma Nizamiyya na Basra ya fi ta Bagdaza girma.

Sai kuma a shekara ta 585 q Salahuddeen Ayyubi ya gina wata makaranta a birnin Qudus. Sai kuma arewacin Afrika inda aka ginda irin wadannan makarantu wadanda suka hada da Jami’ar Zaituna, inda amirai na sarakunan Muwahhidin suka gina makarantu. Sannan a shekara ta 750 aka gina makarantar Nizamiyya a garin Gharnatah.

Daga gabacin daular Musulunci kuma an ci gaba da gina makarantu, wadanda suka hada da Musatansiriyya kusa da kogin Dajla ta Bagdaza, sai kuma makarantar samarakanda.

Sai kuma makarantun shia mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s). An gina makarantun tare da umurnin sarakunan safawiyawa a biranen Esfahana da kuma Shiraz. Daga cikin makarantun akwai ‘Chahar Bagh Esfahanm da makarantar Khan Shiraz, wanda Hakim Mulla Sadra shirazi ya karantar a cikinta.

Sai kuma daga cikin karnukan tsakiya har zuwa yanzu a gina makaranatu da cibiyoyin ilmi da dama. Makarantar Qirawan a garin Fars da wata a Marakash sun jima zuwa karni 11 da suka gabata. Kuma mai yuwa jami’a mafi tsufa a duniyar Musulunci tana can, a cikin mazhabar shia, m ai yuwa Jami’ar Al-Kahira itace jami’a mafi tsofa. Wannan Jami’ar ba’a dade ba, ta yi bikin cika shekaru 1000 da kafuwa.

Wata abu mai jan hankali shi ne, an samarda makarantar Shia ta farko ne  Hauza ta farko a birnin Najfa mai tsarki, sannan har yanzun makarantar tana nan wato kimani shekaru 1000 da suka gabata.

 Makarantar Najaf tana daga cikin manya manyan jamioin shia a duniyar a lokacin har zuwa yanzu. Musayar ilmi da wayewa wani abu ne ta dabi’a. Musulmi sun taka rawa wajen musayar ilmi ko yada shi zuwa wasu mutane. Daga ciki sun yada wayewar musulunci zuwa zuwa girka kamar yanda suka dauko daga garesu. Sannan sun yada shi zuwa kasashen turai musamman a zamanin renaissance wato daga karni  14-17 miladiyya. Banda haka sun yada har da irin ci gaban da suka samu, ko suka bunkasa daga wasu manya manyan kasashen duniya bayan bayyanar addinin musulunci.

Malaman addinin musulunci sun ilmi da sani da kuma wayewa a cikin kanuka kimani 6 da suka yi suna bunkasa shi, wato karnukan zinari, a dai dai lokacinda kasashen turai suke hana muryar malamai tashi.

A lokacin malaman kiristoci ne suke iko da turai, suke kuma Fifita abinda suka fahinta a addinin bisa abinda binciken ilmi ya tabbatar. Wannan riko da addinin ya kai ga, a cikin wadannan karnuka suka kafa kotuna ta hukunta akidun malamai wadanda suka sabawa abinda suka fahinta a addini. Don haka sabawar malaman addini da ilmin bunkasa kwakwalwan dan’adam, da kafirta malaman falsafa yana daga cikin dalilan da suka hana turawa ci gaba a ilmin dabi’a, da sauran fannonin ilmin ci gaba a lokacinda suke iko da turai. Amma addinin musulunci, tun farkon bayyanarsa, ya umurci musulmi su nemi ilmi tabi’a saboda zai taimaka masu a rayuwarsu ta duniya da kuma ta lahira. Zai taimaka masu wajen sanin All..da halittunsa. A hadisi, Manzon All..(s) ya kodaitar da musulmi neman ilmi ko da hakan zai kaisu wuri mafi nesa da inda suke rayuwa.

Don haka musulmi basu dauko ilmi daga kasar Girka da sauran manya manyan kasashen duniya a lokacin ba, kamar ilmin likitanci, da lissafi kawaiba. Sai dai sun gudanar da bincike a cikin wadannan fannonin ilmi suka kuma gano sabbin ilmi, suka kuma kara fadada wadannan fannonin ilmi.

Wasu malaman tarihi suna ganin musulmi sun takaitu da daukar ilmin likitanci na Galen da kuma ra’ayin Ptolemy na ilmin taurari ne kawai, al hali. Amma wadanda suka yi bincike zasu gano cewa, malaman musulmi sun bunkasa wadannan ra’ayoyi da ilmi sun kuma kawo ci gaba wadanda wadan nan malaman girka basu kai garesu ba.

Akwai al-amura da dama a fannonin ilmi masu yawa, wadanda malamai masu bincike musulmi suka fara gano su ko kirkirosu a cikin ilmin tabi’a wadanda suka hada da likitanci binciken taurari da sararin samaniya da sauransu. Kuma a lokacin musulmi sun fi sauran kasashen duniya wayewa a wadan nan fannoni.

Don haka idan muka dauki ilmomin tunani, ko mandiki da falsafa, likitanci, kanikanci, taurari, sanin taurari, lissafi, kimiyar lissafi, wadanda musulmi suka dauko daga kasar Girka daga asali, ba zamu ce da suka shiga hannun musulmi daga cikin karnuika 6 bayan bayyanar addinin musulunci basu ci gaba ba, suna nan kamar yadda aka karbosu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted