Akalla Sojojin HKI 13 Ne Suka Halaka Ko Suka Jikata A Wani Harin Maida Martani A Arewacin Gaza

Dakarun Falasdinawa masu gwagwarmaya da sojojin HKI a Arewacin Gaza, sun halaka akalla sojojin HKI 3 sannan wasu 10 sun ji raunuka, a hare-haren maida

Dakarun Falasdinawa masu gwagwarmaya da sojojin HKI a Arewacin Gaza, sun halaka akalla sojojin HKI 3 sannan wasu 10 sun ji raunuka, a hare-haren maida martani kan sojojin yahudawan a safiyar yau Litinin.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na yahudawa da kuma larabawa da dama suna bada wannan labarin. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa an nuna lokacinda jirage masu saukar ungulu suke kwasar wadanda suka ji rauni zuwa wani asbiti a birnin Yafa Tel’aviv.

Wasu kafafen yada labaran yahudawan, sun nakalto wani babban jami’in sojan kasar ya na cewa bai kamata irin wannan ya faru ba, bayan yaki na tsawon watanni 15. Saboda yakamata a ce sojojin yahudawan suna da cikekken iko da garin Bait Haanun inda abin ya auku.

Wata yar jaridar yahudawan, Etty Landsberg Novo ta yi karin bayani a kan wannan rahoton da cewa, ko wace rana sai an ji, an kashe sojan yahudu, an harbe wani, ko bom ya tashi da wani ko kuma gini ya fada a kan wasu sojojin hayudawan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments